✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fashewar tukunyar gas: Yawan mutanen da suka mutu a Kano ya kai 9

Hukumar NEMA ce ta tabbatar da alkaluman a shafinta na Twitter ranar Talata

Alkaluma na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Gari da ke Kano a yanzu sun kai mutum tara.

Da safiyar Talata ce dai wani abu da ’yan sanda suka ce tukunyar gas ce ta fashe a kusa da wata makaranta inda ya jikkata mutane da dama, wani kuma ya mutu nan take.

Ma’aikatar Jin-kai ta Tarayya ce ta tabbatar da alkaluman, lokacin da take ayyana zuwan Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed a wajen fashewar.

Tun da farko dai ’yan sanda a Jihar sun tabbatar da mutuwar mutum hudu a wajen.

Ma’aikatar ta ce, “Ya zuwa yanzu, an gano gawar mutum tara daga cikin baraguzan ginin da suka danne mutane a kusa da wata makaranta firamare da ke titin Aba Road a Sabon Gari, sakamakon fashewar tukunyar gas.

“Shugaban NEMA, Mustapha Habib Ahmed ya je wajen kuma ya jagoranci aikin ceto mutane.

“Yanzu haka NEMA na jagorantar aikin ceto a wajen da hadin gwiwar sauran hukumomi masu aiki irin nata,” kamar yadda Ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter.