✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwace kujerar tsohon Shugaban Majalisar Kaduna

Aminu Shagali, tsoho Shugaban Majalisar yana kin halartar zamanta

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta bayyana kujerar Dan Majalisa mai wakiltar Sabon Gari, Aminu Abdullahi Shagali a matsayin wadda babu kowa a kanta.

Majalisar ta ce ta dauki matakin ne saboda Aminu Shagali wanda shi ne tsoho Shugabanta ba ya halartar zama ko wasu harkokin Majalisar.

Zaman Majalisar na ranar Talata wanda Mataimakin Shugabanta, Isaac Auta Zankhai ya jagoranta ya kuma tsawaita dakatarwar da ta yi wa wasu ’ya’yanta hudu zuwa wata 12.

Wadanda aka tsawaita dakatarwar da aka yi musu su ne: Mukhatar Isa Hazo, Mazabar Basawa;  Salisu Isa, Mazabar Magajin Gari; Nuhu Goro Shada Lafiya, Mazabar Kagarko; da kuma Yusuf Liman, Mazabar Makera.

Ta kuma umarci akawunta da ya sanar da wadanda matakan suka shafa game da matsayin da zauren Majalisar ya dauka.

A watan Fabrairun 2020 ne Aminu Shagali ya sanar da saukarsa daga kujerar Shugaban Majalisar bisa dalilai na kashin kansa, amma wasu rahotanni na cewa wasu ’yan Majalisar ne ke neman tsige shi.