✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna na neman diyya daga Buhari

Fasinjojin na bukatar gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta daukar musu.

Mutanen da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su na neman Gwamnatin Tarayya ta biya su diyya domin fara sabuwar rayuwa.

Rokon na zuwa ne kusan wata biyu da sakin rukunin karshe na fasinjoji 63 da aka yi garkuwa da su a harin a ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar.

Kazalika, bukatar tasu na zuwa ne sa’o’i 24 kacal bayan da Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dawo da sufurin jirgin a hanyar Kaduna zuwa Abuja, watanni takwas bayan da ta dakatar da ayyukan, biyo bayan harin da ya yi sanadin mutuwar fasinjoji tara.

Sai dai wadanda abin ya shafa, wadanda suka zanta da manema labarai a Kaduna, sun koka kan yadda akasarinsu suka rasa abin dogaro da kai a lokacin da suke hannun ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da su yayin harin.

“Don haka da yawa daga cikinmu mun yi asarar abubuwan da muke yi da kuma hanyar samun kudin shiga. A matsayina na ’yar kasar nan, wadda nake alfahari da kasancewata, ina sa ran gwamnati ta biya mu wani abu,” inji daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Maryam Idris.

“Ina tsammanin za su kawo mana agaji.”

Sun kuma yi ikirarin cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta cika musu alkawuran da ta dauka ba jim kadan bayan ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayan an sake su a watan Oktoba.

Ta kuma ce yawancinsu na fama da ciwon zuciya da rashin lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa.

“A gaskiya, sun tattara bayananmu, cewar za su neme mu. Amma har yanzu babu wanda ya ce mana komai,” cewar Maryam.

“Muna rayuwa ne da jinkan Ubangiji kawai saboda a lokacin da muke tsare, iyalansu sun shiga dimuwa,” inji ta.

Labarin Mariam bai bambanta da na Bala Mohammed ba, wanda ya ce “Babu wanda ya ba mu ko kwabo daya,” duk da cewar wasu daga cikinsu na fama da matsalar rashin lafiya, inji shi.

Ya kara da cewa, “Kalubalen lafiyar da muke fuskanta a yanzu yana da matukar muhimmanci.”

Yayin da ya gode wa Gwamnatin Tarayya da ta kubutar da su, Bala na neman karin agaji daga wajenta.

“Bukatarmu ita ce Gwamnatin Tarayya ta kawo mana dauki domin irin halin da muke ciki a yanzu yana da matukar muhimmanci,” inji shi.

“Ba mu da kudin da za mu je asibiti don kula da lafiyarmu.”