✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinjojin Kamfanin Azman sun makale tsawon sa’o’i 24 a Kano

Sai da misalin karfe 8 na dare sannan aka sanar mana cewa an dage tashin jirgin.

Fasinjojin Kamfanin Jirgin Saman Azman sun shafe sama da awanni 24 suna zaman jiran yin balaguro a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA).

Wasu daga cikin fasinjojin sai da suka kwana a sashin tashi na filin jirgin saboda ba su samu labarin sake shirin tashin jirgin ba sai da yamma.

Yawancin fasinjojin da ke shirin tafiya Abuja da Legas, sun koka da cewa, ya kamata su tashi da karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar, amma ba su samu sanarwar sauya lokacin tashinsu ba sai da misalin karfe 8:00 na dare.

“Na kasance a nan tun ranar Asabar kuma ina tsammanin jirgin zai tashi da karfe 4, amma ma’aikatan kamfanin ba sa ma kusa, ta yadda za su gaya mana halin da ake ciki.

“Sai da misalin karfe 8 na dare sannan aka sanar mana cewa an dage tashin jirgin zuwa yau [Lahadi].

“Wasunmu sun kwana a nan. Wannan babban abin takaici ne,” kamar yadda daya daga cikin fasinjojin mai suna Jamilu Rabiu ya bayyana.

Aminiya ta samu rahoton daga wasu ma’aikatan da ke filin jirgin cewa, kamfanin na fuskantar kalubale da ’yan kasuwar man jiragen sama.

Daya daga cikin ma’aikatan ya ce, fasinjoji da dama da suka hada da mata masu jarirai da kananan yara sun kasance cikin halin kaka-nika-yi na mayar da kansu inda suka fito ko kuma su samu Otal domin su kwana.

“Wasu fasinjoji sun zo nan tun ranar Asabar da misalin karfe 11:00 na safe.

“Akwai wadanda suka yi mana korafin rashin masauki, sannan aka kai su otal.

“Duk da cewa akwai wadanda suka tafi amma wasu suna nan har yau,” kamar yadda wani jami’in Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce.

Sai dai an ruwaito cewa, daya daga cikin ma’aikatan Kamfanin na cewa, matsalar ta samo asali ne sakamakon matsalar fasaha, inda ya tabbatar da cewa fasinjojin za su tashi da misalin karfe 6:30 na yammacin yau [Lahadi].