✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fetur din da ke Neja Delta na ’yan Najeriya ne baki daya —Obasanjo

Obasanjo ya ce albarkatun da ake hakowa mallakin kowane dan Najeriya ne.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce man fetur da ke yankin Neja Delta da ma sauran albarkatun kasar nan, mallakin dukkan ’yan Najeriya ne.

Obasanjo ya yi matarni ne ga kalaman Edwin Clark na yankin Neja Delta, cewa tsohon shugaban kasar ya nuna halin ko-in-kula game da irin illa da hakar mai ke haddasawa a yankin.

Clark, cikin wata wasika da ya rubuta ya zargi Obasanjo da nuna kiyayya ga masu son mallakar albarkatun kasa da ke yankin.

Sai dai a nashi martanin, Obasanjo, ya ce duk wani albarkatun da ake samu kama daga Neja Delta zuwa kowane bangare na Najeriya, mallakin kowane dan Najeriya ne.

Kazalika, Obasanjo ya zargi Edwin Clark da neman samar da wata kasa ne a cikin Najeriya, wanda hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Tsohon shugaban kasar ya ce dukkan mutanen da suka kulla yarjejeniyar sayen danyen man fetur sun yi ne da Najeriya a matsayin kasa ba da yankin Naija Delta ba, yana mai jaddada cewa Najeriya dunkulalliyar kasa ce da babu wanda ya isa ya raba ta, ciki har da raba albarkatun da ke cikinta.

“Idan akwai wata barazanar tsaro a kowane bangare na Najeriya a yau, ciki har da yankin Naija Delta, sojojin Najeriya ne tare da tallafin wasu jami’an tsaro, a matakin Gwamnatin Tarayya, za su magance hakan,” inji shi.

Masu fafutuka a yankin Naija Delta sun dade suna kokarin ganin an mallaka musu albarkatun man fetur din da ake hakowa a yankinsu, inda a wasu lokutan lamarin yakan kai ga kashe-kashe da satar ma’aikatan kamfanonin hakar danyen man.