✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FGC Yauri: An kashe dan sanda, an sace malamai da dalibai

’Yan bindigar sun sace Mataimakin Firinsifal sun harbi dalibai sun sace wasu.

Masu garkuwa da daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Yauri a Jihar Kebbi sun sace Mataimakin Firinisal da wasu malaman makarantar. 

’Yan bindigar sun kashe daya daga cikin ’yan sanda da ke tsaron makarantar, suka harbi wasu dalibai, sannan suka yi awon gaba da dalibai maza da mata.

Majiyarmu a garin na Yauri ta ce, “An kashe daya daga cikin ’yan sanda da ke tsaron makarantar da kuma dalibai maza da mata — makarantar ta maza da mata ce kamar sauran kwalejojin Gwamnatin Tarayya.

“Malamai uku zuwa hudu aka sace, daga cikinsnu har da Mataimakin Firinsifal da wata malama.

“’Yan bindigar sun kuma harbi dalibai biyu, namiji da mace daya; Namijin an harbe shi a mazaunansa, macen kuma a hannu.”

Majiyar ta ce ba a kai ga tabbatar da yawan daliban da aka sace ba, domin fargabar da harin ya haifar ta sa hukumar makarantar kasa gudanar da taron dalibai domin tantance su.

Ta ce tun a makon jiya ake kishin-kishin din shirin kai hari a garin Birnin Yauri, inda makarantar take, wanda hakan ya sa aka girke jami’an ’yan sanda domin tsaron garin.

Da misalin karfe 12:30 na ranar Alhamis kuma mahara dauke da muggan makamai suka kai wa garin hari, inda jami’an tsaro suka gwabza fada da su, lamarin da ya yi sanadin rasuwar dan sandan.

A yayin da ’yan sandan ke musayar wuta da su a kofar shiga makarantar ce wasu daga cikin ’yan bindigar suka fasa katanga suka shiga makarantar ta baya, suka rika yi wa dalibai harbi kan mai tsautsayi.

Majiyar ta ce ’yan bindigar sun dauke motar wani mahaifi da ya kawo dansa rubuta jarabawar JAMB a makarantar, suka dura daliban daliban a ciki, suka wuce da su.

Mun yi kokarin samun karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, amma bai amsa kiran wayar ba, ko rubutaccen sakon.