✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta haramta kunna taken kasar Rasha ko daga tutarta kafin fara wasanni

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta haramta kunna taken kasar Rasha ko daga tutocinta a yayin wasannin da za a buga a wata kasar…

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta haramta kunna taken kasar Rasha ko daga tutocinta a yayin wasannin da za a buga a wata kasar daban.

Matakin na zuwa ne don nuna fushin hukumar kan yadda Rashar ta mamaye kasar Ukraine, wanda ya shiga rana ta biyar.

Tun bayan mamayar Ukraine din dai, kasashe irin su Ingila da Poland da Jamhuriyar Czech da Sweeden suka ce ba za buga wasa da kasar ta Rasha ba.

FIFA dai ta ce za a ci gaba da tattaunawa da sauran kungiyoyin wasanni kan ko za a hana kasar buga wasanni a nan gaba.

A cikin wata sanarwa da FIFA ta fitar da maraicen ranar Lahadi ta ce, “Hukumar gudanarwar FIFA za ta kasance kishin shiri don daukar mataki a kan lamarin.”