✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fikihun soyayyar ma’aurata

Assalamu alaykum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaykum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga ci gaban bayani kan ilimin soyayya domin ma’aurata su fahimci wannan babban jigo na rayuwar aure kuma su dabbaka da aikatar da soyayya cikin huldodinsu da zamantakewar aurensu:

Hukuncin soyayyar ma’aurata a shari’a
Idan muka bibiyi da yawa daga cikin ayoyin Alkur’ani da Hadisan Manzon Rahma (Sallalahu Alaihi Wasallam), da labaran magabatanmu (Allah Ya kara yarda a gare su), za mu fahimci cewa yana daga cikin kyautatuwa da ingantawa da cikar kamalar mutum ya kasance mai soyayya ne mai kuma bayyanar da soyayyarsa ga abin da yake so.

Ba wani waje da addini ya yi hani ga soyayya ko bayyanar da ita, sai dai a wurare da yawa an nuna yin hakan abin so ne kuma abin yabawa ne.

Kalmar soyayya ayar Kur’ani ce, kuma Hadisan Manzon Allah cike suke da kyawawan misalai da ayyukan soyayya da kauna.

Soyayya a Alkur’anil Karim Kalmar soyayya ko kauna sun bayyana a wurare 90 cikin Alkur’ani Mai girma, amma abin sha’awar shi ne, a duk inda suka bayyana suna bayani ne a kan sakamakon da ke bin soyayya, wato shi ne riko ga abin da ake so din.

A kan haka muna iya fahimtar cewa duk wata soyayyar da ba riko kyakkyawa a cikinta, to ba za ta yi alfanu ba.

A cikin aya ta 21 cikin Suratul Rum, Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana cewa, Shi ne Mai sa soyayya a tsakanin mata da miji ma’auratan juna.

“Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta muku matan aure daga kawunanku, domin ku natsu zuwa gare su; sannan ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku…”

Daga wannan aya mai albarka za mu iya fahimtar cewa, natsuwa da juna ita ce farkon tubalin ginin soyayyar auratayya, kuma ma’aurata za su natsu da juna ne kadai idan sun kasance sun bi dukkan dokokin da Allah Madaukaki Ya shar’anta musu game da rayuwa kuma musamman game da zamatakewar aure.

Nagartacciyar soyayya mai cakude da tausayi ce za ta biyo bayan wannan natsuwa.

Idan muka lura, ma’auratan da ba su natsu da juna ba su ne kullum cikin rikici da rashin kwanciyar hankali da yawan fadacefadace.

Idan kuwa da su duka za su koma ga Allah gaba daya su mai da al’ama’rinsu gare Shi, to za su samu natsuwar zuci wacce a hankali za ta gina musu kammalalliya kuma cikakkiyar soyayya a tsakaninsu.

Kamar yadda babban malami Ibnul Kayyim ya fada: “Duk wani so da zai janye mutum daga son Allah (rashin yin da’a ga Allah ko saba wa dokokinSa Subhanahu Wa Ta’ala), to azaba ne. Amma son da ya jawo son Allah shi ne cikakken so, tsarkakakke.”

Soyayya a Sunnar Manzon Allah (SAW)
Haka kuma idan muka bibiyi sunnonin Manzon Allah (SAW), za mu samu misalai da yawa kan yadda ake soyayya da yadda ake bayyanar da soyayya.

Idan mutum yana bin yadda Annabi (SAW) ya yi rayuwar auratayyarsa, zai fahimci cewa Annabi (SAW) ya kasance kwararre wajen iya aikatar da soyayya salo-salo ga matansa (Radiyallahu Anhunna), kuma hakan na matukar dadada musu zuciya da kwantar musu da hankali da cika musu natsuwar zuci.

Haka kuma su ma Uwayen Muminai sun kasance ba su yi kasa a gwiwa ba wajen nuna masa tasu soyayyar.

An tambayi Annabi (SAW) wa ya fi so cikin mutane? Ya ce A’isha (Radiyallahu Anha). Kuma ya ce game da Uwar Muminai Khadija (Radiyallahu Anha): “Na cika da soyayyarta!”

An karbo daga Anas (Radiyallahu Anhu), cewa Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam), ya ce: “Abubuwan da aka soyantar gare ni daga abubuwan wannan duniya su ne mata da turare mai dadin kanshi, kuma Sallah ta kasance sanyin idanuwa gare ni.”

Sannan a wani ingantaccen Hadisi, Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ruwaito cewa Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba mu ga wani abu da ya dace ga mutum biyu masoyan juna ba illa aure.”

Wato aure shi ne zai cika soyayyarsu kuma ya inganta ta, amma idan ba auren, to soyayyarsu ba za ta amfane su ba, tana ma iya kai su ga sabon Allah (Azza Wajallah).

Soyayya daga fahimtar magabata

Babban malami Ibnul Jawziyyu ya yi wannan bayani game da soyayya a cikin littafinsa: Cuta da Magani:

“Yana daga cikin cikar mutumtakar namiji son matan aurensa domin Allah Ya albarkaci bayinSa da wannan so, har ma Ya fada, a Aya 28 cikin Suratul Nisa’i’ ‘Kuma an halicci mutum da rauni (game da mata)’.”

Kuma Manzon Allah ya kasance mai nuna soyayya ga matansa, haka ma da yawan Annabawan Allah, irin Annabi Ibrahim da Annabi Sulaiman da Annabi Dawud (Alaihimus Salam) duk sun so matan aurensu.

Ya kara da cewa: “Son matan aure ko abin da hannun daman mutum ya mallaka (kuyangi) abu ne mai kyau domin yana kawo alfanu kuma a kan haka ne Allah Ya shar’anta aure domin tsare gannai don haka wannan so ne abin yabawa a wurin Allah haka kuma a wurin mutane.”

Haka nan babban malami Ibn Hazm ya yi gamammen bayani a cikin littafinsa mai suna Zoben Tantabara cewa:

“Soyayya ba abar kyama ba ce a addini ba a kuma haramta ta ba a shari’ance domin kowace zuciya a Hannun Allah take.”

Haka kuma ya kara da cewa “ba sha’awa ce kadai soyayya ba, amma dai ita ce masomin soyyayar.”