✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filato ta Kudu: Kotu ta tabbatar da zaben Sanata Daduut

Kotun ta tabbatar da Sanata Nora Daduut din a zaman da tayi a ranar Litini.

Kotun sauraron kararrakin zaben Majalisun Tarayya da na jiha da ke zama a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, ta tabbatar da Sanata Farfesa Nora Ladi Daduut ta jam’iyyar APC, a matsayin wadda ta lashe zaben cike gurbin kujarar Majalisar Dattawa ta Filato ta Kudu, da aka gudanar a ranar 5 ga watan Disamba, 2020.

Kotun ta kuma tabbatar da Sanata Nora Daduut din a zaman da tayi a ranar Litini.

Kotun ta yi bayanin cewa koken George Daika na jam’iyyar PDP, da suka yi takarar wannan zabe, da ya shigar a gabanta ba shi da tabbatatun shaidu, don haka ta yi watsi da karar.

Tun da farko George Daika ya kalubalanci Hukumar Zabe ta Kasa kan bayyana Sanata Daduut a matsayin wadda ta lashe zaben a gaban wannan kotu.