✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Finalissima: Italiya da Argentina za su kara a Wembley

Gasar tsakanin zakarun nahiyoyin biyu za ta bai wa ‘yan kallo damar kallon zakarun biyu a fili guda suna fafatawa.

Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA ta sanar da filin wasa na Wembley da ke birnin Landan a matsayin farfajiyar da za a doka wasa tsakanin zakarar Turai Italiya da zakarar America wato Argentina mai rike da kambun Copa America.

Karawar wadda za ta gudana ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, Italiya ta samu zarafin kaiwa matakin ne bayan doke Ingila a wasan karshe na EURO cikin watan Yulin bara a bugun fenariti.

Haka kuma a bangare guda ita ma Argentina ta iya kaiwa matakin bayan itama ta lallasa Brazil da kwallo 1 mai ban haushi.

A watan Satumban bara ne hukumomin CONMEBOL da na UEFA suka tattauna tare da dawo da kwarya-kwaryar gasar da aka yi wa lakabi da ‘‘Finalissima’’.

An tsara gasar za ta rika gudana tsakanin zakarun nahiyoyi gabanin tabbatar da ita a watan Disamban bara, yayin da kuma UEFA ta sanar rana da kuma lokacin gudana da ita a ranar Talatar da ta gabata.

Sanarwar da UEFA ta fitar ta ce sabuwar gasar tsakanin zakarun nahiyoyin biyu zai bai wa ‘yan kallo damar kallon zakarun biyu a fili guda suna fafatawa.

Ita dai wannan gasa da ma akan gudanar da ita tsakanin zakarun nahiyoyin biyu amma aka dakatar da gudanar da ita tun daga shekarar 1993.

Irin wannan haduwa ta karshe da aka gudanar ita ce haduwar Argentina da Denmark a wancan lokaci inda tawagar Argentina karkashin jagorancin Diego Maradona ta lallasa Denmark.