✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fintiri ya yi gargadi kan yaduwar coronavirus a zagaye na biyu

Gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana damuwarsa kan yadda cutar coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa yayin da mahukuntan lafiya na duniya suka…

Gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana damuwarsa kan yadda cutar coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa yayin da mahukuntan lafiya na duniya suka ayyana cewa guguwar annobar ta kado a zagaye na biyu.

Gwamnan ya bayyana damuwarsa ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta bakin ma Sakataren Yada Labaran fadar gwamnatinsa, Humwashi Wonosikou.

Sanarwar ta ce, “Bayan tabbatar da cewa annobar coronavirus tana kan zagaye na biyu, Najeriya da ma duniya baki daya, dole ne mu sake saka wasu matakan don tabbatar da tsaron lafiya da kuma rayukan al’ummarmu,” inji gwamna Fintiri.

Ya ce gwamnatinsa ya za ta sake shimfida sabbin dokoki ciki har da wadanda ake amfani da su domin dakile yaduwar cutar.

Ganin yadda cutar ta janyo koma baya ga tattalin arziki, Fintiri ya ce gwamnatinsa ba ta da niyyar sake saka wata sabuwar dokar zaman kulle da za ta kuntata wa al’umma.

A cewarsa, abin da ya fi dacewa shi ne jama’a su yi taka-tsan-tsan wajen kiyaye dokoki da matakan kare kai daga kamuwa da cutar.

Gwamnan ya ja hankalin mutane a kan amfani da takunkumi, wanke hannu a-kai-a-kai da sunadarin tsaftace hannu ko kuma a karkashin ruwa mai gudana da kuma ba da tazara ta hanyar kaurace wa shiga taron jama’a da bai zama tilas ba.

Gwamnan ya bukaci masu wuraren shakatawa a kan su bi doka wajen rufe wuraren da misalin karfe 10 na dare a kullum.

Kazalika, Gwamna ya yi wa jama’ar jihar fatan alheri game da Sabuwar Shekara ta 2021 da ake maraba da ita.