✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fira ministar Birtaniya ta yi murabus

Fira Ministan Birtaniya, Liz Truss, ta ajiye mukaminta, kwana 44 bayan da fara aiki.

Fira Ministan Birtaniya, Liz Truss, ta ajiye mukaminta, kwana 44 bayan da ta fara aiki.

Liz Truss ta ce ta yi murabus ne saboda gazawarta wajen sauke nauyin da aka dora mata na kawo sauyi da saukin rayuwa ga al’ummar Birtaniya.

Truss, wadda ta gaji Boris Johnson, wanda ya yi murabus bayan rikicen siyasa da suka dabaibaye shi, ta ce, an zabe ta ne domin, “kawo sauyi daga wannan matsala.”

Ta ajiye aiki ne washegarin jawabinta ga majalisar ministoci, inda ta ce ita, “jaruma ce ba raguwa ba.”

Ta ce, duk da gazawarta wajen kawo sauyin da ake bukata, amma “mun amince da dokar makamashi.”

Sanarwar ajiye aikin nata ta ce, “Na karbi aiki a matsayin Fira Minista a lokacin da kasar nan ke cikin babban kalubalen tattalin arziki da kuma matsaloli a kasashen duniya.

“Iyalai da harkokin kasuwanci na cikin damuwa na cikin matsin kan yadda za su biya bukatunsu.”

Mukin Misis Truss ya kasance cike da rudani a bangaren kasuwanci, tun bayan da aka sanar da karamin kasafi a watan Satumba.

A makon jiya ne ta sallami tsohon shugaban gwamnati Kwasi Kwarteng tare da soke was daga sauye-sauyen harajin da Truss ke shirin ragewa, matakin da ya kara haifar da karin matsala.