✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firaiministan Isra’ila ya kai ziyarar ba-zata Masar

Ziyarar ita ce irinta ta farko da wani babban jami’in Isra'ila ke kai wa kasar Masar.

Firaiministan Isra’ila Naftali Bennett ya kai wata ziyarar ba-zata Masar inda kasashen biyu ke fatan bude sabon babi a inganta huldar diflomasiyya.

Firaiminista Bennet ya bayyana fatan ganin samun hadin kan Shugaba Abdel Fattah al-Sisi don karfafa dangantaka da kuma hada kai a samar da tsaron yankunan biyu kamar yadda aka amince a wata yarjejeniya da kasashen suka cimma tun a shekarar 1979.

Ziyarar ta kasance irinta ta farko da wani babban jami’in Isra’ila ke kai wa kasar Masar.

Ägypten Scharm el Scheich | Treffen Ministerpräsident Israel Bennett und Präsident al-Sisi

Hakazalika rahotanni sun tabbatar da isar Yarima Mohammed bin Zayed al-Nahyan na Abu Dhabi a Masar inda ake sa ran za su gana da Shugaba al-Sisi a wani katafaren wurin shakatawa da ke Sharm El-Sheikh.

Gidan Rediyon Jamus da ya ruwaito daga Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce babu dai bayani kan dangantakar haduwar shugabannin a lokaci guda.

Sai dai daga bisani rahotanni sun ce Shugaba al-Sisi da Bennett da kuma Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi sun yi tattaunawa irinta ta farko tun bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta daidaita dangantakarta da Isra’ila shekaru biyu da suka gabata.

Shugabannin sun tattauna kan makamashi da samar da abinci da kuma tsaron yankin — musamman dangane da Iran da kuma batun farfado da yarjejeniyar nukiliyarta da ta kulla da kasashen yammacin Turai a 2015.

Masu aiko da rahotanni sun ce kasashen uku wani bangare ne na sahun kasashen Larabawa da ke kawance da Isra’ila da ke neman dakile tasirin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.