✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Firaiministan Sudan, Abdalla Hamdok ya yi murabus

Hamdok ya bayyana cewa ya yi iya kokarinsa na ganin ya kare kasar daga tsunduma cikin bala’i.

Firaiministan Sudan, Abdalla Hamdok ya yi murabus watanni bayan hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulki da sojojin kasar suka yi.

Wannan lamari dai shi ne makamancinsa na farko a bayan nan tun bayan da kasar ta rika tangal-tangal a yunkurinta na komawa tsarin mulkin dimokuradiyya biyo bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Murabus din na zuwa ne a yayin da kuma sojoji suka rika amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin hadaka ta soji da farar hula.

Koda yake sojojin su saki Hamdok a ranar 21 ga watan Nuwamba karkashin wata yarjejeniya wadda a cikinta ya amince ya shirya zaben shugaban kasa a tsakiyar shekara ta 2023.

A yayin gabatar da jawabi ga al’ummar kasar ta kafar talabijin ranar Lahadi, Hamdok ya bayyana cewa, ya yi iya kokarinsa na ganin  ya kare kasar daga tsunduma cikin bala’i.

Bayanai sun ce sa’o’i kadan kafin jawabin da Hamdok ya yi ne jami’an tsaro suka kashe wasu masu zanga-zanga uku, lamarin da ya sanya adadin mutanen da aka kashe tun bayan juyin mulkin zuwa 57.

Ana iya tuna cewa dubun dubatar mutane ne suka rika fitowa domin kalubalantar gargadin da mahukunta suka yi kan cewa ka da wanda ya fito da nufin gudanar da tarzomar adawa da gwamnatin hadaka da ta hada sojoji da fararen hula a kasar.