✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Firaministan Sri Lanka ya yi murabus

An gudanar da zanga-zangar kin jin gwamnatin Firaminista Mahinda Rajapaksa.

Firaministan kasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, ya yi murabus bayan da magoya bayansa dauke da sanduna da kulake suka kai wa masu zanga-zangar adawa da mulkinsa hari.

Kasar ta sha fama da karancin wutar lantarki, abinci, man fetur da magunguna a sakamakon fada wa matsalar tattalin arziki mafi muni, tun bayan samun ‘yancin kai, lamarin da ya janyo zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Kakakin Rajapaksa, Rohan Weliwita, ya ce firaministan ya aike da wasikar ajiye aiki zuwa ga kaninsa, shugaba Gotabaya Rajapaksa, abin da ya share fagen kafa sabuwar gwamnati.

Tun kafin barkewar tarzomar, babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta ce ba za ta shiga wata gwamnati da ke da iyalan gidan Rajapaksa a matsayin jagora ba.

Murabus din firaministan na nufin cewa an rushe majalisar dokokin kasar kenan, kuma za a gudanar da wani sabon zabe.

Rahotanni sun rawaito cewa a ranar Litinin ne, rikici mafi muni ya tashi a babban birnin kasar Colombo, a lokacin da magoya bayan iyalan Rajapaksa suka afka wa masu zanga-zanga.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Tuni aka saka dokar ta baci ba tare da bata lokaci ba a birnin na Colombo, wadda daga bisani suka fadada ta zuwa gaba daya sassan kasar mai yawan mutane kimamin miliyan 22.