✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiya: Ya wajaba United ta gama a sahun ’yan ukun farko —Ronaldo

Ronaldo ya ce bai zo firimiya don karkare kaka a matsayin na shida ba.

Fitaccen dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya ce ya zama wajibi kungiyarsa ta dage don ganin ta kare Firimiyar Ingila ta bana a cikin sahun ’yan ukun farko.

Ronaldo ya yi ikirarin cewa zai zama abin kunya idan har kungiyarsa ta gaza kammala gasar firimiyar bana a sahun ‘yan ukun saman teburi dai dai lokacin da mai horarwa Ralf Rangnick ke kokarin dawo da tawagar turbar nasara biyo bayan rashin abin kirki a wasanni da dama da ya kai ga sauya manaja.

Kalaman na Ronaldo na zuwa bayan shan kayen da United ta yi a hannun Wolves da ya janyowa kungiyar caccaka inda dan wasan ke cewa a zuciyarsa ya na ganin tabbas za su iya kammala firimiya matsayin na 2 ko na 3 ko da basu iya dage kofin a wannan karon ba.

Babu dai wata gagarumar nasara tun bayan maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer da Rangnick ya yi inda yanzu haka kungiyar ke matsayin ta 7 a teburin Firimiya tazarar maki 22 tsakaninta da Manchester City jagora.

Sai dai Ronaldo na Portugal mai shekarau 34 wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Ballon d’Or har sau 5 ya ce dolensu ne matsayin ‘yan wasan kungiyar su sauya tunani tare da jajircewa don ganin basu yi abin kunya a karshen kaka ba.

A cewar Ronaldo bai zo firimiya don karkare kaka a matsayin na 6 ko na bakwai ba fatansa shi ne sake dage kofin firimiya tare da tsohuwar kungiyar tasa kuma har zuwa yanzu bai karaya ba.