✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Ingila ta fitar da gwarazan ‘yan wasa 11 mafi kwazo

Sunan Ronaldo ya shiga jerin sunayen gwarazan 'yan wasa 11 da Hukumar Kwallon Kafa ta Firimiyar Ingila ta fitar.

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta fitar da jerin gwarazan ‘yan wasa 11 daga kungiyoyi daban-daban mafi kwazo a gasar firimiyar ta bana.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ce ke kan gaba ta fuskar yawan ‘yan wasanta da suka shiga jerin, inda ‘yan wasa shida suka samu gurbi a cikin ‘yan wasa 11 da hukumar ta fitar.

Kungiyar Manchester City da ta lashe gasar ce ka sahu na biyu da ‘yan wasanta uku suka shiga ciki, sai Chelsea da Man United da aka samu mutum daya kowannensu.

Ga jerin ‘yan wasan kamar haka:

Alisson — Liverpool

Trent Alexander-Arnold — Liverpool

Virgil van Dijk — Liverpool

Antonio Rudiger — Chelsea

Joao Cancelo — Manchester City

Kevin De Bruyne — Manchester City

Thiago Alcantara — Liverpool

Bernardo Silva — Manchester City

Sadio Mane — Liverpool

Cristiano Ronaldo — Manchester United

Mohamed Salah — Liverpool.­