Fitacciyar mai karanta labarai a gidan talbijin na AIT Nkiruka ta rasu | Aminiya

Fitacciyar mai karanta labarai a gidan talbijin na AIT Nkiruka ta rasu

Marigayiya Nkiruka Udom
Marigayiya Nkiruka Udom
    Abbas Dalibi

Shaharariyar ‘yar jarida mai karanta labarai a gidan talabijin mai zaman kansa na AIT, Nkiruka Udom ta rasu

Nkiruka Udom ta rasu ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2020 a Legas bayan an yi mata tiyata a wani asibiti, amma aka samu tangarda.

Kafin rasuwarta Nkiruka ta yi fice sosai wajen karanta labarai a gidan talabijin na AIT kana wakiliyace a sashen labaran nishadi a tashar ta  AIT.