✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Fitattun fina-finan Kannywood da suka fi daukar hankali a bana

Aminiya ta zakulo wasu fina-finai da suka fi shahara a masana’antar Kannywood a bana.

Shekarar 2021 ta dan zo da ci gaba a masana’antar Kannywood bayan matsalolin da ta fuskanta a bara a dalilin bullar annobar covid-19.

A bana, an yi fina-finai da dama a masana’antar ciki har da masu dogon zango da suka yi fice har suka ta kawo muhawara a tsakanin mutane.

Wannan ya sa Aminiya ta zakulo wasu fina-finai da suka fi shahara a masana’antar Kannywood a bana.

Ka yi na yi

A tarihin sinimar Film House da ke Ado Bayero Mall Kano, fim din ‘Ka yi na yi’ ne fim din da ya fi tara kudi, inda ya tara jimillar kudi Naira 5,464,500.

Fim ne na barkwanci da aka tsara shi a matsayin cigaban shirin ‘Kalan dangi’ da aka yi a bayan.

A fim, an tara manyan jarumai irinsu Ali Nuhu da Sani Danja da Yakubu Mohammed da Musa Mai Sana’a da Sadiq Sani Sadiq da Aminu Shariff Momoh da Maryam Yahaya da sauransu.

Fim ne na barkwanci da cuta da damfara da cin amana.

Abubakar Bashir Maishadda ne ya shirya, Dauda Kahutu Rarara ya dauki nauyi, sannan Ali Gumzak ya bayar da umarni.

Fastar fim din ‘Ka yi na yi’

Labarina

A watan Janairun bana ne daraktan fim din ‘Labarina’ Malam Aminu Saira ya sanar da cewa za a dakatar da haska fim din na wani lokaci, sannan za a sanar da inda za a cigaba da haska fim din daga baya.

Sanarwar ta jawo ce-ce-ku-ce, inda masoya shirin suka yi tashar Arewa24 ca cewa sun samu matsala ne.

Daga baya daraktan ya zanta da Aminiya, inda ya nuna cewa ba a fahimci sanarwar ba ce, inda ya fayyace cewa an gama zango na biyu, sai sun kammala daukar zango na uku da na hudu za su sanar da cigaba da haskawa.

A July 2 ga watan Yunlin bana aka cigaba da haska shirin a tashar ta Arewa24, sannan aka fara dan taba-ka-lashe a tashar YouTube.

Fim din ya samu karbuwa sosai domin har irin mutanen da ba kasafai suke kallo wasan Hausa ba, suna kallo kuma sukan yi sharhinsa a kafafen sadarwa.

Har yanzu shirin na ‘Labarina’ yana cigaba da daukar hankalin masu kallo.

Akai jarumai irinsu Nafisat Abdullahi da Nuhu Abdallah da Daddy Hikima da sauransu.

Fim din kamfanin Saira Movies ne, Aminu Saira da Nazir M. Ahmed da Nazifi Asnanics suka shirya, sannan Malam Aminu Saira ya bayar da umarni.

Fastar Labrina

Gidan Badamasi

Gidan Badamasi fim din barkwanci ne da ake yi wa lakabi da maganin hawan jini saboda yadda nishadantar da jama’a ta hanyar sanya su dariya.

Za a cigaba da haska zango na 4 a Alhamis 6 ga Januarun badi ne kamar yadda daraktan shirin Falalu Dorayi ya sanar bayan sun kammala daukar shirin a Zariya na Jihar Kaduna a watan jiya.

Akwai jarumai irinsu Adam A. Zango da Falalu Dorayi da Hadiza Gabon da Ummi Shehu da Ado Gwanja da sauransu.

Fim din kamfanin Dorayi Films & Distribution ne, sannan Falalu Dorayi ya bayar da umarni.

Sanda

Bayan nasarar da aka samu, ko ake cigaba da samu a shirin ‘A duniya’ inda jarumi Daddy Hikima, wanda aka fi sani da Abale ya yi fice a ciki, sai jarumin ya shirya fim dinsa mai suna ‘Sanda’

‘Sanda’ fim ne da aka shirya akan dabanci da soyayya, inda matashin dan daba zai kamu da soyayya, sannan ya kuduri aniyar kare soyayyarsa.

Akwai jarumai irinsu Daddy Hikima da Rukky Alim da

’Yan mata da yawa ne suke son matashin, wanda Daddy Hikima ne a matsayin Sanda, sannan mahaifiyarsa da yake ‘Umma’ a fim din tana so ya yi aure.

A duniya

Fim din ‘A duniya’ har yanzu yana daukar hankali musamman matasa, inda a yanzu taken ‘in da rabbana’ da amsar ‘babu wahala’ ke cigaba da yaduwa a tsakanin matasa.

Har malamai sai da suka yi tsokaci akan taken fim din.

Shirin wanda Tijjani Asase ya dauki nauyi an shiryasa ne akan yanayin rayuwar matasa da harkar shaye-shaye da dabanci da yadda ake gudanar da su a boye a cikin al’umma.

Sanusi Dan Yaro ya ba da umarni.

Wuf  

Fim din ‘Wuf’ shi ma ya ja hankalin mutane musamman yadda aka sa masa da suna da wani sabon yanayi da zamani ya zo da shi, inda ake cewa an yi wuf idan matashiya ta aura dattito ko matashi ya aura tsohuwa.

Fim din ya kunshi soyayya cin miji da mata da yaudara.

Jaruma Ummi Rehab ce ta ja shirin, sannan akwai Abdul M. Shareef da mawaki Lilin Baba, wanda shi ne ya dauki nauyin fim din.

Alfa Zazee na ya bayar da umarni.

Sauran finafinan da suka dauka hankali akwai irinsu Izzar so da Haram da Farin Wata da finafinan talabijin na Arewa24 irinsu Dadin Kowa da Kwasa 90 da suka kara samun masu kallo a bana.