✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun mutum 10 da cutar Kurona ta kashe a duniya

Cutar Kurona (COVID-19) wadda ta  fara  bayyana a garin Wuhan na kasar China a Disamban bara, ta ci gaba da yaduwa a kasashen duniya kamar…

Cutar Kurona (COVID-19) wadda ta  fara  bayyana a garin Wuhan na kasar China a Disamban bara, ta ci gaba da yaduwa a kasashen duniya kamar wutar daji inda ta hallaka fitattun mutane da suka yi fice a fannoni daban-daban a duniya kama daga fagen ilimin kimiyya da na addini da wasanni da bangaren nishadantarwa da kuma fagen siyasa. Cutar ba ta bar babba ko yaro ba, kamar yadda ba ta bar mace ko namiji ba. Mun zakulo fitattun mutum 10 da cutar ta kai su Lahira a sassan duniya kamar haka:

1. Li Wenliang (33)

Li Wenliang masanin cututtuka da ke aiki a matsayin likita a Babban Asibitin Wuhan. Shin ne fitaccen mutum na farko da cutar Kurona ta kashe.  Shi  ne ya fara gargadi kan yiwuwar barkewar wata cuta da take kama da murar mashako ta SARS tun a watan Disamban bara, wadda ita ce a karshe aka sanya wa suna COBID-19.Bayan ya fallasa batun cutar da aka rika yadawa daga baya, sai ’yan sanda suka kama shi a ranar 3 ga Janairun bana suna tuhumarsa da shara karya a Intanet. Daga baya Li ya koma wurin aikinsa, amma sai ya harbu da cutar daga wani marar lafiya inda ya rasu a ranar 7 ga Fabrairun bana yana da shekara 33. Daga baya kwamitin bincike na Jamiyyar Gurguzu ya wanke shi daga tuhumar da ake yi masa aka nemi afuwan iyalansa tare da janye gargadin da aka yi

2. Stanley I. Chera (70)

A ranar Asabar da ta gabata ce, cutar ta Kurona ta hallaka Mista Stanley I. Chera, wani babban aminin Shugaban Amurka Donald. Kafar labarai ta The Real Deal, da ke bayar da labaran harkokin gine-gine a  birnin New York ce ta bayyana rasuwar wannan fitaccen dan kasuwa mamallakin kamfanin gine-gine na Crown Ackuisitions. Chera yana daga cikin wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawar kudi ga kamfe din da ya kawo Shugaba Trump gadon mulki.

Tun ranar 29 ga Maris Trump ya ambaci kamuwa da cutar da amininsa Chera mai shekara 70 ya yi, cutar da ta kashe Amurkawa sama da dubu 20 da 600 zuwa tsakiyar ranar Lahadin da ta gabata kamar yadda Jami’ar Johns Hopkins mai tattara bayanan wadanda cutar ta kashe a duniya ta bayyana.

Trump ya taba bayyana abokin nasa Chera a gangamin Grand Rapids a Michigan, a shekarar 2019 da “daya daga cikin manyan masu harkar gine-gine da harkokin gidaje kuma masana harkar gidaje a duniya.”

3. Seyyed Hadi Khosroshahi (81)

Kasar Iran ce kasar da ta fi rasa manyan mutane a wannan annoba. Ta rasa ’yan majalsar dokoki da manyan malamai da masana da manyan sojoji. Daga cikin manyan malaman da ta rasa har da Seyyed Hadi Khosroshani, malami kuma masanin diplomasiyya. Shi ne tsohon Jakadan Iran a Fadar Fafaroma. Khosroshahi yana daga cikin manyan malaman makarantar Shi’ar nan ta Kom kuma ya taba zama wakilin Ayatollah Khomeini a Ma’aikatar Musulunci da Al’adu, jim kadan da samun nasarar Juyin Juya-Halin Musulunci na Iran a 1979. Kuma bayan shekara biyu a can ne aka tura shi Fadar Fafaroma a matsayin Jakada. Cutar Kurona ta yi ajalinsa a ranar 27 ga Fabrairun bana.

4. Seyyed Mohammad Mirmohammadi (71)

Babban Mashawarcin Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, Seyyed Mohammad Mirmohammadi yana daga cikin manyan ’yan siyasar Iran, wakili ne a Majalisar Koli ta Mulkin Iran. Kuma ya taba zama dan Majalisar Dokokin Iran ta shida da ta bakwai daga mazabar Kom. Mohammad ya taba zama mamba a Babban Kwamitin     Jam’iyyar    Islamic

Republic Party. Kuma Shugaban

Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa a zamanin shugabancin Ayatollah Ali Khamenei da Hujjatul Islam Ali Akbar Hashemi Rafsanjani. Kuma ya zama Babban Sakataren Jam’iyyar Islamic Cibilization Party. Ya rasu ranar 2 ga Maris da ya gabata sakamakon cutar Kurona.

5. Janar Nasser Shabani (62)

Janar Nasser Shabani yana daga cikin manyan kwamandojin Rundunar Juyin Musulunci (IRGC) ta Iran. Shi ne aka ce ya yi amfani da mayakan Houthi a kasar Yemen wajen kai wa rijiyoyin man Saudiyya hare-hare da makamai masu linzami. Ya fara aikin soji ne a 1982 lokacin yakin Iran da Iraki, kuma ya rika samun karin girma har ya zama daya daga cikin fitattun kwamandojin Rundunar IRGC, sakamakon rawar da ya taka a fagen yaki. Ya taka rawa a fafatawar da ake kira Operation Mersad,   daga   baya   ya rubuta littattafai da dama a kan yakin. A shekarar 2011 ne ya gaji Shugaban Jami’ar Imam Hussain inda ya zama daya daga cikin na’iban Sansanin Tharallah.

A shekarar 2018, ya fadi ta kafar watsa labaran Iran cewa Rundunar IRGC ce ta umarci mayakan Houthi a Yemen su kai hari kan manyan rijiyoyin man Saudiyya biyu da ke Bab al-Mandab. Ya rasu ranar 13 ga Maris dalilin cutar Kurona.

6. Ayatollah Reza Mohammadi Langroudi (91)

Ayatollah Reza Mohammadi Langroudi yana daga cikin manyan malaman Shi’a Imamiyya a Iran, wanda hakan ya sa ya kai matsayin Ayatollah. Shi ne wakilin Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei a garin Langroud. Kuma shi almajirin Ayatollah Hossein Borujerdi ne da Ayatollah Ruhollah Khomeini da Ayatollah Mohammad-Taki Bahjat Foumani. Ya taka rawa sosai a lokacin zanga- zangar da ta jawo Juyin Juya-Halin Musulunci a Iran a 1979. Ya zama limamin Juma’a na wucin-gadi a Langroud da Amlash.Ya rasu yana da shekara 91 sakamakon harbuwa da cutar Kurona a ranar 7 ga Maris da ya gabata.

Sauran fitattun  Iraniyawa  da cutar ta kashe su ne Fatemeh Rahbar mai shekara 56 da Mohammad-Reza Rahchamani ma shekara 67 dukkansu wakilan majalisar dokokin Iran da sauransu da dama.

7. Ayatollah Reza Mohammadi Langroudi (81)

Dan siyasar kasar Kongo. Tsohon hafsan soja da ya zama Janar na  farko  a  kasar  kuma ya zama Shugaban Kasa da Firayi Ministan Kasar Kongo- Brazzabille daga 1977 zuwa 1979. Shi ne Snugaban Jam’iyyar Rally for Democracy and Development (RDD), wadda a karkashinta ya zama Firayi Minista daga 1993 zuwa 1996. Daga shekarar 1997 zuwa 2007 ya yi gudun hijira daga kasarsa. Kuma a ranar 30 ga Maris ne cutar Kurona ta kashe shi.

8. Mahmoud Jibril el-Warfally ( 67)

Dan siyasar kasar Libya ne da ya rike mukamin Firayi Ministan Gwamnatin Rikon Kwarya na wata bakwai da rabi a lokacin Yakin Basasar Libya, inda ya Shugabancin Majalisar Mika Mulki (NTC) daga 5 ga Maris zuwa 11 ga Oktoban shekarar 2011. Babban na hannun daman marigayi Shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi ne kafin ya juya masa baya ya jagorancin tawayen da ya kawo karshen mulkin Gaddafi na fiye da shekara 30. Shi ne Shugaban babbar jamiyyar siyasar Libya ta National Forces Alliance. Ya rasu ne a wani asibiti a Alkahira da ke Masar ranar 5 ga Afrilu sakamakon harbuwa da cutar Kurona.

9. Alfa Saadu (68)

Alfa Sa’adu fitaccen likita ne dan Najeriya da ke zaune a Ingila. Mahaifinsa Ahaman Pategi tsohon Minista ne a zamanin su Sardauna, Firimiyan tsohuwar Jihar Arewa. Cutar Kurona ta kashe shi ne bayan ya yi jinya wa mutane da dama da cutar ta kama. Ya rasu ne a ranar 31 ga Maris yana da shekara 68.

10. Manu Dibango (86)

Mawaki Manu Dibango da ke zaune a Faransa a kusan daukacin rayuwarsa ya rasu ne a ranar 24 ga Maris a wani asibitin birnin Paris na Faransa sakamakon harbuwa da cutar Kurona. Manu Dibango, dan asalin kasar Kamaru ne da tauraruwarsa ta fara haskakawa a fagen waka a 1972 lokacin da ya saki wata wakarsa mai suna “Soul Makossa.”

Sauran fitatun mutanen da cutar Kurona ta hallaka sun hada da tsohon Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid Lorenzo Sanz da Janar Aytac Yalman tsohon Kwamandon Sojin Turkiyya da Akibishop din cocin Katolika na kasar Ukraine, Stephen Sulyk da tsohon Firayi Ministan Somaliya Nur Hassa Hussein da aka fi sani da Nur Adde da tsohon jagoran addinin Yahudu na kasar Isra’ila (Rabbi) Eliyahu Bakshi-Doron da Alhaji Suleiman Achimugu, tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na Najeriya (PPMC) da ma’aikacin talabijin na Zimbabwe, Zororo Makamba da jarumar fim Lee Fierro da jarumi Mark Blum da dan wasan barkwanci na Japan, Ken Shimura da fitaccen mai kamfanin dinke-dinken suturar nan na Italiya Sergio Rossi da sauransu da dama.