✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun ‘yan kwallo 5 da suke auren bakaken fata

Yayin da ake fama matsalar wariyar launin fata, wasu 'yan kwallo na auren bakaken fatar.

Duniyar kwallon kafa ta dade tana yaki da nuna wariyar launin fata, amma duk da haka wasu na ci gaba da nuna kyama ga bakaken fata.

Amma wasu ‘yan kwallon a wajensu abun ba haka ya ke ba, domin kuwa har auratayya ta shiga tsakaninsu.

  1. ‘Buhari ya fi shekara 40 yana zuwa Landan a duba lafiyarsa’
  2. Kwalara ta kashe mutum 479 a Najeriya —NCDC

Aminiya ta rairayo muku wasu fitattun ’yan kwallo da ke auren bakaken fata kamar haka:

1. Mason Mount

Mason Mount da matarsa Chole Weallenans-Watts

Dan wasan gaba na Ingila da Chelsea, Mason Mount na auren masoyiyarsa, Chole Weallenans-Watts wadda mawakiya ce.

2. Thomas Meunier

Thomas Meunier da matarsa Deborah Panzokou

Dan wasan kungiyar Borrusia Dortmund da kasar Belgium, Meunier ya auri budurwarsa da suka dade tun daga makaranta, Deborah Panzokou. Sun haifi yaro guda daya tun a 2015.

3. Clement Lenglet

Clement Lenglet da matarsa Estelle

Dan wasan bayan na Barcelona da kasar Faransa, Lenglet ya kasance mutum ne wanda baya bayyana abin da ya shafi rayuwarsa a zahiri.

Amma an gano yana tare da Estelle, sai dai ba a san tsawon wane lokaci suka shafe suna tare ba.

4. Julian Weigl

Julian Weigl da matarsa Sarah Richmond

Dan wasan kasar Jamus da kungiyar Borussia Dortmund, Weigl ya auri masoyiyarsa mai suna Sarah Richmond, a kasar Portugal.

Dan wasan ya aureta tana da shekara 23 a duniya, yayin da shi kuma ya ke da shekara 25 a duniya.

5. Daniel Gosling

Daniel Gosling da matarsa Ashley Simmons

Dan wasan Ingila da kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, Daniel Gosling ya auri masoyiyarsa Ashley Simmons.

Wadannan fitattun ‘yan kwallon sun auri mata bakaken fata duk da shahararsu a duniya.

Wasu daga cikinsu sun yi auren ne don nuna rashin goyon baya ga wariyar launin fata a tsakanin ‘yan Adam da ake nuna wa a harkar kwallon kafa.