✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fitila ta kona jariri kwana daya da haihuwarsa

Wutar jikin wata fitila da ta fado wa wani jariri mai kwana daya a duniya ta yi sanadin konewarsa a fuska da kafafu a birnin…

Wutar wata fitila da ta fado wa wani jariri mai kwana daya a duniya a birnin Kalaba na jihar Kuros Riba ta yi sanadin konewarsa a fuska da kafafu.

Fitilar ta kuma kona wasu sassan jikin jaririn jim kadan da zuwansa duniya.

Wata ganau a lokacin da abun ya faru mai suna, Misis Stella Aluka ta ce iftila’in dai ya fadawa jaririn ne a falon dakin da aka haife shi saboda mahaifiyarshi ba za ta iya biyan kudin haihuwa a asibitin ba.

A cewarta, fitilar dake haska dakin ce wacce take amfani da kananzir ta yi bindiga tare da kona shi, lamarin da ya yi sanadiyyar samun raunuka da dama a jikinsa.

Tuni dai aka garzaya da jaririn asibitin Victoria a birnin Kalaba inda yake ci gaba da samin kulawa.

Stella ta ce, “Mahaifiyar yaron ta je wani gidan karbar haihuwa ne domin ta haihu a can saboda ba za ta iya biyan kudin asibiti ba. Kwatsam sai fitilar ta fado masa a dakin da aka haife shi.

“Ba zan iya misalta irin wahala da zafin da jaririn yake sha ba ko kuma na mahaifiyarshi a halin yanzu,” inji ta.