✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fityanul Islam za ta kaddamar da asusun gina gidan marayu ranar Alhamis

Shugaba Buhari ne zai kasance babban bako a wajen taron

Kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya ta cewa za ta kaddamar da wani asusu na musamman a ranar Alhamis mai zuwa domin gina gidan marayu na Sheikh Ibrahim Inyass da Cibiyar Koyar da Sana’o’i a Zariya, Jihar Kaduna.

Kungiyar ta ce tana sa ran gidan ya samar wa dubban marayun da hare-haren ta’addanci suka raba su da iyayensu a fadin kasar nan matsuguni.

A sanarwar da ya rattaba wa hannu, Mataimakin Sakatare na kungiyar, wanda kuma shi ne Shugaban babban kwamitin shirya taron na kasa, Dokta Musa Muhammad Imam, ya ce za a kaddamar da asusun ne a lokacin babban taron kungiyar na shekara-shekara wanda zai gudanar a dakin taro na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da ke Abuja.

Sanarwar ta kuma ce za a gudanar da zaben shugabannin kungiyar na kasa a kashegarin ranar taron.

Dokta Imam ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai kasance babban bako na musamman, yayin da shugaban taron shi ne dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.

Fityanul Islam ta kuma ce babban mai kaddamarwa shi ne dan takarar Shugaban Kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sannan babban bako mai jawabi shi ne Babban Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari.

“Ita dai kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya (FIN), an kafa ta ne a 1962 a Kano a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Inyass Al-Kaulahi (rta), kuma tun daga lokacin ta kasance mai taka muhimmiyar rawa wajen da’awar addinin Musulunci ta hanyar daruruwan makarantun ta da ke cikin Najeriya da sauran kasashen yankin Afrika ta Yamma,” inji sanarwar.