✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fiye da mutane 3,000 sun harbu da Coronavirus rana guda a China

An sanya kwarya kwaryar dokar kulle a birnin Jilin.

Hukumomin lafiya a China sun sanar da samun mutane dubu 3 da dari 4 da suka harbu da cutar Covid -19  a cikin sa’o’i 24, adadin da ya ninka na ranar Asabar.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa wannan lamarin ya tilasta dokokin kulle a yankunan da annobar ta fi shafa, a yayin da kasar ke kokarin yakar matsala mafi rauni a cikin shekaru 2.

Wani jami’in ma’aikatar lafiya ya sanar a ranar Lahadi cewa an sanya kwarya kwaryar dokar kulle a birnin Jilin, inda aka hanadaruruwan mutane fita daga gidajensu, a yayin da aka rufe ilahirin birnin Yanjin da ke iyaka da Koriya ta Arewa.

China, inda cutar ta fara bulla a shekarar 2019 ta ci gaba da daukar tsauraran matakai don dakile annobar, inda ta aiwatar da dokokin kulle masu tsauri,da kuma gwaji ba kakkautawa.

Amma bullar nau’in cutar na Omicron  a baya bayan nan yana kalubalantar matakan da hukumomi ke dauka.