✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fiye da rabin yara a Ukraine sun koma ’yan gudun hijira – UNICEF

UNICEF ya ce hakan ba karamar illa zai yi ga kananan yaran ba a nan gaba

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce hare-haren da Rasha take kai wa kasar Ukraine ya sa fiye da rabin yaran kasar sun zama ’yan gudun hijira.

A cewar asusun cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, “Wata daya bayan fara yaki a Ukraine, sama da yara miliyan 4.3 ne – fiye da rabin yaran kasar da yawansu ya kai miliyan 7.5 – ne suka rasa muhallansu.”

Alkaluman dai a cewar Asusun sun hada da yara sama da miliyan 1.8 da aka tsallaka da su zuwa makwabtan kasashe da kuma wasu miliyan 2.5 da yanzu haka yakin ya daidaita a cikin kasar.

“Yakin na daya daga cikin yake-yaken da suka daidaita yara tun bayan Yakin Duniya na Biyu,” inji Catherine Russell, shugabar UNICEF.

Ta yi gargadin cewa hakan zai yi matukar illa ga kananan yaran a shekaru masu zuwa, inda rayuwarsu ke ci gaba da zama cikin mawuyacin hali.

Tun a karshen watan Fabrairun 2022 ne dai kasar Rasha ta kaddamar da kai hare-hare kan Ukraine, bisa yunkurinta na shigar kungiyar kawance tsaro ta NATO.

Miliyoyin mazauna kasar ne suka koma ’yan gudun hijira a sakamakon haka, wasu da dama suka fice daga kasar.