✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani 4,000 sun yi kaura daga Kudu zuwa Kaduna

Wasu daga cikinsu sun tako a kasa bayan an koro su daga Kudancin Najeriya

Akalla makiyaya 4,000 ne suka yi kaura zuwa Jihar Kaduna sakamakon barazarar da suke fuskanta a yankunan da suke zama a Kudancin Najeriya.

Dubban makiyayan sun sauka ne a garin Ladduga na Karamar Hukumar Kachia, da ke zaman matattarar Fulani makiyaya da aka raba da muhallansu a Kudancin Kaduna.

Hakar Aminiya ta jin ta bakijn Ardon Ladduga, Ruguni Pate ba ta cimma ruwa ba, amma wani mazaunin Ladduga, Mohammed Iliya, ya ce Fulanin sun dawo garin bayan an koro su daga Kudancin Najeriya, sun iso ne a motoci wasu kuma a kafa tare da dabbobinsu.

Mohammed, “Abin akwai ban takaici da tausayi, in ka ga halin da suke ciki, musamman mata da kananan yara, sai ka zubar da hawaye.

“Wasu an kashe su, an kone gidajensu, an kashe musu dabbobi. Yanzu yawancinsu a fili suke kwana don ba mu da inda za mu tsugunar da su, sannan muna tsammanin karin wasu na nan tafe,” inji Mohammed.

Ya ce Hukumar Ba da Agaji ta Jihar Kaduna (SEMA) ta ziyarci garin inda ta dauki bayanan makiyayan, amma yana kira ga gwamnati da ta taimaka musu da kayan tallafi.

Mataimakin Daraktan Ayyuka na SEMA, Hussaini Abdullahi, wanda ya ziyarci Ladugga, ya ce hukumar na ci gaba da aikin daukar bayanan makiyayan su sama da 4,000.

Mun tuntubi Shugaban Hukumar, Abubakar Hassan ta waya, amma ya ce ba zai iya bayar da cikakken bayani ba sai an gama daukar bayanansu.

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyayay ta Miyetti Allah, Reshen Jihar Kaduna, Haruna Usman Tugga, ya shaida wa Aminiya cewa zai ziyarci Laddugga domin ganawa da Fulanin da kuma ganin halin da suke ciki.