✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani sun yafe wa mutanen Jos kisan matafiya

Shugabannin Fulanin sun yi alkawarin ba za a dauki fansa ba.

Shugabannin al’ummar Fulani a yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya sun ce sun yafe wa mutanen Jihar Filato da suka kashe Fulani matafiya kusan 30 a garin Jos ranar Asabar.

Shugabannin Fulanin da suka fito daga yankin Kudu Maso Yammacin sun bayyana hakan a ranar Juma’a ta bakin Shugabansu, Alhaji Kabiru Muhammed.

Ya sanar da afuwar ce a ke garin Akure a lokacin da Gwamnatin Jihar Filato ta kai wai Gwamnatin Jihar Ondo ziyarar ta’aziyya game da rasuwar matiyan da kuma mika mata wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin.

“Gwamnatin Jihar Filato ta nemi a yafe kuma mun yafe. Allah Yana yafe wa mai yafiya.

“Ina tabbatar muku cewa mun yafe wa kowa saboda a samu kwanciyar hankali da kuma dorewar Najeriya.

Babu daukar fansa —Fulani

“Muna kuma tabbatar muku cewa ba za a dauki fansa ba, kuma mutane sun yi farin ciki da ganin ’yan uwansu su dawo cikinsu. Najeriya na gaban da kowa ko bukatar wani,” inji Alhaji Mohammed.

Gabanin sanar da yafiyar Fulanin, Mataimakin Gwamnan Jihar Filato, Farfesa Sonny G. Tyoden, wanda ya jagoranci tawagar masu ta’aziyyar ya roki jama’ar Jihar Ondo da su yafe wa ’yan Jiharsa abin da ya faru.

Tyoden ya ba su tabbacin cewa, “Akwai mutanen da aka tsare a kan harin kuma tabbas doka za ta yi aiki a kansu.

“Jihar Filato na maraba da kowa kuma gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayukan mazauna jihar ko ta raga wa masu neman tayar da fitina ba.”

A nashi bangaren, Sarkin Wase, Dokta Muhammad Sambo Haruna, wanda ke cikin tawagar masu ta’aziyyar, ya roki iyalan wadanda harin ya ritsa da su cewa su dauki lamarin a matsayin kaddara. Ya roki Allah Ya karbi ‘shahadar’ wadanda suka rasa rayukan nasu.

Da yake mayar da jawabi, Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya ce samun labarin harin ke da wuya, Gwamna Rotimi Akeredolu ya kira takwaransa na Filato, Simon Lalong domin jin halin da mutanen jihar ke ciki, sannan ya je kasuwar kara ya jajanta wa al’ummar Fulani

An tare Fulani ne a yankin Gada-Biyu da ke garin Jos, bayan sun fito daga taron addini a Jihar Bauchi, aka yi wa akalla mutum 27 daga cikinsu kisan gilla, aka jikkata wasu sama da 20, wasu kusan 20 kuma suka tsira.

Lamarin ya jefa jihar da sauran Najeriya cikin dar-dar da tsoron harin daukar fansa, har ta kai ga gwamnatin Filato ta sanya dokar hana fita na sa’a 24 a garin Jos, ta kuma tsare wasu mutum 20 bisa zargin su da hannu a kisan.