✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulanin Kudancin Kaduna ‘yan asalin yankin ne —Sanata Laah

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Sanata Danjuma Tella Laah ya bayyana cewa Fulanin  Kudancin Kaduna ‘yan asalin yankin kamar sauran kabilun. Sanatan Laah…

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Sanata Danjuma Tella Laah ya bayyana cewa Fulanin  Kudancin Kaduna ‘yan asalin yankin kamar sauran kabilun.

Sanatan Laah ya bayyana haka ne a taron zaman lafiya da Kungiyar Fulani Makiyaya ta Kasa (Miyetti Allah) reshen Jihar Kaduna ta gudanar a garin Kafanchan don bayar da gudummuwa kan hanyoyin da za a bi don dawo da zaman lafiya a yankin.

Sanatan, wanda ya yi kira ga daukacin kabilun yankin da suka rika girmama juna, ya ce abin takaici ne iyaye da kakanni su zauna lafiya a lokacin da ake cewa babu ilmi amma kuma zaman lafiya ya tabarbare a lokacin da ake ganin an waye.

Danjuma Laah, wanda ya janyo hankalin dukkanin bangarorin kan su guji kiran juna da sunayen da ba su dace ba, ya tunatar da su irin yadda aka yi zaman lafiya a yankin a baya, inda ya ce babu wani ci gaba da yankin zai samu matukar babu zaman lafiya.

Taron, wanda ya zo bayan makwanni biyu da gudanar da irinsa tsakanin kabilun Fulani da Katafawa da Hausawa a Karamar Hukumar Zangon Kataf, yana nuna irin kokarin da kowane bangare ke yi don shawo kan matsalolin da suka addabi yankin.

Yayin da yake jawabi tun da farko, Shugaban Taron, Dakta Salim Umar, ya yi kira ga dukkannin bangarorin da su guji boye masu laifi a cikinsu.

Ya ce maimakon haka, su rika fito da su suna mika wa hukumomin da suka kamata don hukunta su.

Dakta Salim ya kuma shawarci taron da ya kafa kwamitin hadaka na zaman lafiya da na samar da tsaro da sa ido da zai kunshi dukkanin bangarorin Fulani da sauran kabilun yankin da abin ya shafa domin gudanar da ayyukan da za su samar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Da yake jawabin maraba, Shugaban Kungiyar ta Miyetti Allah na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman Tugga, ya jawo hankalin makiyaya da su guji tura kananan yara zuwa kiwo musamman a damina don gudun shiga cikin cikin gonakin manoma.

Ita ma da take nata jawabin, Babbar Mataimakiyar Shugaban Hukumar Wanzar da Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna wacce ta wakilci Gwamnatin Jihar, Dakta Priscilla Ankut ta bayyana samuwar zaman lafiya mai dorewa a yankin a matsayin babban burin Gwamnatin Jihar.

Ta yi kira ga sauran kungiyoyi a yankin da su yi koyi da kungiyar ta Miyetti Allah wajen shirya irin wadannan tarukan akai-akai.

A cikin takardar bayan taro da aka fitar jim kadan bayan kammala zaman, an zartar da wasu kudurori guda takwas da suka hada da yin kira ga kowace masarauta a Kudancin Kaduna da ta yi kokari wajen shirya kwatankwacin taron zaman lafiyan da aka shirya a Masarautar Atyap.

Takardar, na dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar ta Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman Tugga da Mai Magana; da Yawunta, Ibrahim Bayero Zango da Shugaba; da Sakataren Kungiyar Na kudancin Kaduna, Abdulhamid Musa; da Shu’aibu Mogauri Usman  a ranar asabar a garin Kafanchan.

Sun yi kira ga manoma da su guji toshe labin shanu na cikin gida da hanyoyin wasa da wasa da ya ratsa ta yankin, da hana kananan yara kiwo da damina, sannan da daukar alwashin komawa ga zaman lafiya irin ta da tsakaninsu da kowa a yankin.

A karshe takardar da yaba wa rundunar kiyaye zaman lafiya, musamman ta ‘Operation Safe Haven’ bisa kokarinta na kamanta gaskiya a aikinta.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da ta tarayya da su tallafa wa al’ummar Fulanin da suka rasa dabbobinsu da rugagensu da sauran kayayyakin yau da kullum.

Taron ya samu halartar jami’an tsaron sojoji na Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya na ‘Operation Safe Haven’ da Rundunar ‘Yan Sanda da DSS da wakilin Ardon Fulanin Najeriya da Shugabannin Miyetti Allah na Jihohin Nasarawa da Filato da sauran kungiyoyin Fulani da Mobgal Fulbe Development Association da Gan Allah da sauransu.