✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fursunoni 10 za su tafi jami’a a Kano

17 daga fursunonin sun rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) ta 2020.

10 daga cikin fursunoni da ke zaman wakafi a Jihar Kano na neman gurbin karatu a Jami’ar Karatu daga Gida ta Najeriya (NOUN).

Kwanturolan Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya (NPS) na Jihar Kano, Suleiman Suleiman ya ce 17 daga fursunonin da ke jihar na cikin daliban da suka rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) ta bana.

Ya ce wasu daga cikin masu neman gurbin karatun jami’ar sun riga sun kammala karatun sakandare kafin a kawosu cibiyar.

Ya kara da cewa masu zaman wakafin da za su yi jarabawa za su yi ne a makarantar ‘ya’yan ma’aikatan NPS da ke gidan yarin Goron Dutse a birnin Kano.

Don haka ya yi kira ga jama’a da su guji tsangwamar tsoffin fursunonin da suka kammala zaman wakafinsu suka dawo cikin al’umma.

“Mu daina nuna musu kyama domin kada su koma aika abind a tun farko ya sa aka kai su gidan yari”, inji Suleiman.