✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fursunoni sun ta da bore a babban gidan yarin Kano

Tarzomar dai ta barke ne kan wata tabar wiwi da aka shigo da ita cikin gidan ranar Alhamis.

Fursunoni a babban gidan yarin Kano dake unguwar Kurmawa da yammacin Alhamis sun ta da tarzoma kan shigo da wasu miyagun kwayoyi.

Aminiya ta gano cewa tarzomar ta barke ne a gidan jim kadan da yin bude baki, bayan da fursunoni suka ta da kayar baya kan kwace wata tabar wiwin da aka shigo musu da ita.

Hukumar dake Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) reshen jihar Kano ta tabbatar da lamarin, amma ta ce jami’anta sun yi ta maza wajen dakile yunkurin.

Kakakin hukumar reshen jihar Kano, Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka kafa kwamiti don gano yadda tabar wiwin ta shiga gidan.

Ya ce, ”Wani ne ya shigo da tabar wiwi ga fursunoni amma jami’anmu suka kwaceta, shine suka ta da tarzoma a kan lallai sai an basu.

“Tuni ma mun kafa kwamiti domin gano yadda aka yi tabar ta shigo gidan; ko a cikin irin abincin bude bakin da ake kawowa fursunoni ne aka sako ko kuma da jami’anmu aka hada baki.

“Tarzomar ba ta da alaka da kowanne irin yunkuri na balle gidan yarin ko na guduwa,” inji shi.

To sai dai wasu na zargin cewa fursunonin sun yi yunkurin balle gidan ne domin guduwa ne don nuna bacin ransu kan irin abincin da ake ba su da azumi, duk kuwa da irin tarin gudunmawar da suka karba daga masu hannu da shuni.

Amma kakakin ya musanta wannan zargin inda ya ce ba shi da tushe ballantana makama.

Gidan yarin Kurmawa dai wanda ya haura shekara 100 da ginawa shine babban gidan yari a jihar Kano kuma yana bayan Fadar Sarkin Kano.