✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fyade: Gwamnatin Tarayya ta karrama matashiyar Kano da ta kirkiro manhaja

Gwamnatin Tarayya ta karrama matashiyar Kano wadda ta kera manhajar da za ta rika bayar da damar shigar da korafe-korafen fyade ba tare da tsangwama…

Gwamnatin Tarayya ta karrama matashiyar Kano wadda ta kera manhajar da za ta rika bayar da damar shigar da korafe-korafen fyade ba tare da tsangwama ba.

Ministan Sadarwa da Fasahar Inganta Tattalin Arziki, Dokta Isa Ali Pantami ne ya gabatar da takardar karamcin ga Sa’adat Aliyu a ofishinsa da ke birnin Abuja.

Dokta Pantami ya ce Sa’adat ta samu wannan lambar yabo ta Gwamnatin Tarayya domin yaba wa bajintar da ta yi na kirkirar wannan sabuwar manhaja mai bayar da damar shigar da bayanai kan cin zarafin mata.

Ministan ya nemi Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwar Zamani ta NITDA a kan ta hada hannu da matashiyar domin inganta ayyukanta da kuma dora ta a kan turbar da ta dace daidai da tanadin dokokin kasar.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, Sa’adat ta yi murna da wannan lambar yabo da ta samu.

“Ina alfahari da wannan karamci da kuma yabawa da gwamnatin tarayya ta yi min ta hannu Ministan Sadarwa da Fasahar Inganta Tattalin Arziki, Dokta Isa Ali Pantami,” a cewarta.

A makon da ya gabata ne Sa’adat Aliyu wacce ’yar asalin jihar Kano ce ta yi tashe musamman a dandalan sada zumunta bayan ta bayyana cewa ta kirkiri wata manhaja  mai suna ‘Helpio’ kuma aka kaddamar da ita a rumbun manhaja na wayoyi.

Sa’adat ita ce shugabar kamfanin Sharmrok Innovation mai kirkire-kirkiren fasaha kuma mai gwagwarmayar ci gaban mata fannin kirkira.