✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ga gwamnonin jihohin da ke fama da harin ’yan bindiga

Gaisuwa mai yawa da fatar alheri ga ma’aikatan wannan jarida mai farin jini. Bayan haka ina so ku  ba ni dama in ba da takaitacciyar…

Gaisuwa mai yawa da fatar alheri ga ma’aikatan wannan jarida mai farin jini. Bayan haka ina so ku  ba ni dama in ba da takaitacciyar shawara ga gwamnonin jihohin da ke fama da hare-hare ’yan bindiga da garkuwa da mutane, kamar su Katsina da Kaduna da Sakkwato. A gaskiya yakar ’yan ta’adda har a kai ga nasara a wannan lokaci a kuma kasa irin Najeriya zai yi matukar wuya, domin ni haifaffen Jihar Zamfara ce kuma duk irin makirci da kisisinar da ke cikin yaki da wannan ta’addanci mun ji kuma mun ga zahiri, saboda dama an ce naka shi yake ba da kai.

Amma cikin ikon Allah idan kuka dauki matakin sulhuntawa da su ta hanyar sarakunan su Fulanin tsakani da Allah, to tabbas akwai yiwuwar a samu zaman lafiya irin yadda jiharmu ta Zamfara ta samu saukin wannan ta’addanci da kashi 80 cikin 100.

A karshe ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya dawwamar da zaman lafiya a jihohinmu na Arewa maso Yamma da Najeriya baki daya amin.

Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan-Ɓaure (Dan Kishin Talaka), Jihar Zamfara 08139177665. Daminar bana: Jama’a na neman dauki a Dambam

Assalamu alaikum Edita.Talakawa masu ginin kasa a Karamar Hukumar Dambam a Jihar Bauchi suna cikin wani hali na neman taimako. Tun lokacin da aka shiga watan Agusta, al’umma da dama suka fara fuskantar rushewar gidaje, wadansu kuma na cikin fargaba inda a halin yanzu matsalar ta wuce yadda ake zato domin ta zamo hantsi leka gidan kowa. Da wuya ka jera gidaje uku ba ka samu daya a cikinsu ya fuskanci matsalar rushewa ba, wanda hakan ke tilasta wa mutane da dama ficewa daga muhallansu. Kuma wani abin tausayawa  shi ne da yawa daga ciki talakawa ne masu fama da abincin bakinsu. Saboda haka muke kira ga gwamnatinmu mai albarka a karkashin jagoranci Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir, cewa da ta turo wakilanta domin gane wa da idonsu girman wannan matsala, tare da taimaka mana domin mu gyara muhallanmu. Allah Ya sa sakon mu ya kai ga gwamnatinmu ta Jihar Bauchi, kuma ta share mana hawaye cikin gaggawa, amin.

Daga Hussaini Abba Dambam, Karamar Hukumar Dambam, Jihar Bauchi 0802081473.

Shekara 28 masu albarka a Jigawa Tarin Allah

Shekara 28 ba dakika takwas ba ne, ba minti takwas ba ne, ba awa takwas ba ne, ba kwana takwas ba ne, ba wata takwas ba ne.

Shekaru ne dai-dai har guda ashirin da takwas. A cikin wannan mako ne ranar 28, ga Agusta, Jihar Jigawa ta yi bikin cika shekara 28. Duk da karancin shekarun wannan jiha ta girme ni fiye da wata takwas. A madadin Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Jigawa muna mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar Jihar Jigawa, Allah Ya karo shekaru masu albarka.

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja 08100229688.

Matsalar tsaro a Najeriya

Aminiyata, mu ’yan Najeriya muna cutuwa da wasu munanan ra’ayoyi, manufofi da akidoji na kasashen ketare. A kan haka hukuma tana asarar makudan kudi da rayukan jami’an tsaro da farin kaya. Ya kamata ta sa ido ga masu dakon wannan tsiyar. Masu hikima sun ce, “Raba matarka da yawo ko kuma yawo ya……”

Daga Usman Abdullah Abuja 08062277369.

Shawara ga ’yan Najeriya

Assalam Editan Aminiya. Don Allah ina son in gaya wa ’yan uwana ’yan Najeriya, mu ji tsoron Allah a koyaushe mu roki Allah Ya ba mu zaman lafiya.

Daga Alhaji Bilya Doya Boy, Zauro Jihar Kebbi, 07067467444.

Jinjina ga Gwamnan Zamfara

Assalamu alaikum Edita. Da fatar kuna lafiya amin. A gaskiya mu al’ummar Jihar Zamfara muna yi wa Allah godiya da zabin da Ya yi mana, da kuma samun gwarzon Gwamna. Allah Ya yi jagora Ya kare shi daga dukkan sharri, amin.

Daga Maman Aliyu Tsafe.

Mun yaba kokarin jami’an tsaro

Yunkurin juyin juya-hali da wadansu maciya amanar kasar nan suka yi shirin aiwatarwa ya gamu da cikas. Hakan kuwa ya faru ne bisa ga jajircewar jami’an tsaro na kasar nan. Muna yaba wa jami’an tsaronmu. Allah Ya kara musu kaifin basira Ya kuma ba su ikon dakile duk wasu kungiyoyi masu son cin amanar kasarmu da cin amanar shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari, amin.

Daga Suleyman Sani Suleyman 08032300925.

Sakon ban-gajiya ga  Baba Buhari

Salam zuwa ga gwamnatin Baba Buhari jagaba shugaban talakawa maganin kwarin azzalumai. Edita ka isar min da sakon ban-gajiya zuwa ga baban talakawa. Kuma ya yi kokari ya farfado mana da matatar mai ta Kaduna. A karshe ina yi masa fatar alheri. Allah Ya kara wa Baba Buhari lafiya da mu baki daya.

Daga Abu Yazyd Loko Nation Wite 09052526237.

Tunatarwa ga Gwamnatin Jigawa

Salam Edita. Ka isar min sakona ga Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar, kyan alkawari cikawa. Sabon titinmu daga Maigatari zuwa Kumsa ko da man zancen ’yan siyasa ka yi mana da ashe jiya ne da yanzu an gama.

Daga Gambo Khashifu Diginsa 09068054350.

Kira ga ’yan majalisa masu kishin Arewa

Assalam jaridarmu ta AMINIYA. Ina yi wa al’ummar Musulmi Barka da Sallah. Don Allah ina kira ga ’yan majalisarmu masu kishin Arewa da shugabanmu mai adalci, su dubi Allah su mayar da ni aikina na soja, shi na sani kuma shi na iya. Shekara 12 ina gida, ga iyaye ga iyali ga ’yan uwa,

Daga Abubakar Muhammed Jos 08144949685.

Cin zarafin direbobi a Jihar Imo

Assalamu alaikum. Don Allah Shugaban Kasa ko ka san irin wulakanta direbobi da ake yi a shingen iyakar Jihar Imo ya kai akalla ka ba da Naira 100. Amma fa duk get sai ka ba da Naira 200. Wani ma sai ya kai Naira 500 dole ko su fasa maka taya ko gilashin mota da sauransu ko ma su taba lafiyarka. Don Allah Gwamnan Imo da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ku tsawatar domin hakkinku ne a matsayinku na shugabannin al’umma. Bissalam Allah Ya sa a dace amin.

Daga Salahuddeen Aliyu Umar Kwa Dawakin Tofa, Kano.08144805146.

Taya murna ga iyalan Magajin Garin Daura

Assalamu alaikum Edita. Ina taya iyalai da al’ummar garin Daura murnar kubuta da dawowar Mai girma Magajin Garin Daura. Allah Ya kiyaye al’ummar Musulmi baki daya.

Daga Tasi’u M. Sani Argungu Tashan Aina Argungu 08069148895

Gyaran hanya: Kira ga Masari

Salam Edita. Don Allah muna roko ga Gwamna Aminu Masari ya taimaka wa al’ummar, Sabuwar Kofa da Lambobi da Malali zuwa Kasuwar Gwari da hanya.

Daga Ibrahim Malam, 07062903579.

Ta’aziyyar  Danmadamin Daura

Sallam Edita. Ku mika mini sakon ta’aziyyar Abdurrahaman Danmalam  Danmadamin Daura. Gaskiya mun yi babban rashi ga masoya da iyalansa da al’umar kasa baki daya kan gudunmawarsa ga yankin Arewa. Allah Ya gafarta masa zunubansa baki daya, amin.

Daga Umar A. Umar Mazoji, Matazu LGA, Jihar Katasina 07054286772.

A fahimci juna tsakanin sojoji da ’yan sanda

Salam Edita. Allah Ya kawo fahimtar juna a tsakanin sojoji da ’yan sandan Najeriya game da abin da ya faru a Karamar Hukumar Ibbi. Kuma ’yan sandan da suka rasu, Allah Ya jikansu.

Daga Aliyu Korau Bajari, Gishirin Hassan Karamar Hukumar Ibbi, Jihar Taraba. 07013322949

Ta’azziyar Bashir Musa Liman

Assalamu alaikum. A mika sakon ta’aziyyata ga ’yan uwa da abokan arziki, bisa rasuwar dan uwa abokin aiki. BASHIR MUSA LIMAN. Ina addu’ar Allah Ya yi masa rahama.

Daga JOURNALIST El-Ishak Yusif Maiyaki Kano 07033008320.

Kira ga Gwamnatin Kebbi

Salam Editan Aminiya. Don Allah ka mika min kirana ga gwamnatin Jihar Kebbi kan ta yi wa Allah ta kalli al’ummar Karamar hukumar Bunza ta taimaka ta ba mu Abdulkadir Bawa Bunza (A.K) a matsayin Shugaban Karamar Hukumar Bunza, Allah Ya sa a dace.

Daga Abdussamad Aliyu Bunza, Shiyyar Fada, 09031860413.

Duk  wanda ya yi  Gwamna kada a zabe shi  sanata 

Ina kira ga ’yan  Najeriya  don Allah duk  wanda ya yi  Gwamna kada mu zabe shi  a sanata.  Saboda duk  gayyar  tsiya ce  ba su da anfani  sai barnar da suka yi  suke karawa.  Wasalam.

Daga Adamu Sulaiman Kaugama  Sauna Kano