✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gabriel Boric: Dan shekara 35 ya zama shugaban kasa a Chile

Boric ya yi babbar nasara ta ba zato ba tsammani a kan abokin hamayyarsa.

Titunan Santiago sun barke da murna a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da Gabriel Boric ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a kasar Chile.

Bayanai sun ce Boric ya yi babbar nasara ta ba zato ba tsammani a kan abokin hamayyarsa a wata takara mai cike da rudani da aka fafata.

Sanarwar da Hukumar Zaben kasar ta fitar wadda ta bayyana Boric mai shekaru 35 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya sanya dubban magoya bayansa gudanar da bukukuwa a titunan birnin Santiago.

Boric ya samu kashi 56 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin karawarsa, Antonio Kast ya samu kashi 44, kuma tuni ya amsa shan kayen zaben.

Hakan ya sanya masu bikin murnar nasarar suka sahef tsawo awanni suna amfani da kayan wasan wuta da rawa a kan tituna domin bayyana farin cikinsu.

Shugaban ’yan adawar kasar, Kast wanda ya jagorancin kawancen da ya hada da na ’yan ra’ayin rikau ya taya Boric murnar nasarar da ya samu.

Kast ya ce daga yau Boric ya zama zababben Shugaban kasar Chile saboda haka ya dace kowa ya mutunta shi da bashi goyan bayan da yake bukata domin kai kasar zuwa ga ci.

Gabriel Boric wanda yake jagorantar kawancen da ya kulla da jamiyyar gurguzu ta Chile zai karbi ragamar jagorancin kasar a watan Maris da za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.