✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gada ta karye a Amurka ana daf da ziyarar Shugaban Kasa a wajen

Rahotanni sun ce ko a watan Satumban bara sai da injiniyoyi suka yi aikin duba lafiyar gadar.

Wata gada ta rushe a birnin Pittsburgh na Jihar Pennsylvania a Amurka ana daf da ziyarar da Shugaban Kasar, Joe Biden, ya shirya kaiwa birnin.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne gabanin ziyarar Shugaban, wacce dama makasudinta shi ne a kan gabatar da wani kuduri da ke neman a kai wa gine-gine a kasar daukin gaggawa.

Shugaba Biden dai ya sha nanata cewa galibi gine-ginen kasar, musamman na gidaje da hanyoyi sun tsufa matuka, kuma suna bukatar sabuntawa.

Rahotanni sun ce akalla mutum 10 ne suka samu raunuka a sanadin karyewar gadar, wacce kuma daga bisani ta yi sanadiyyar fashewar wata tukunyar gas a wajen.

Kakakin Fadar Shugaban Amurka ta White House, Jen Psaki , ta ce an sanar da Shugaba Biden batun karyewar gadar, kuma duk da haka zai kai ziyarar kamar yadda aka tsara.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a dai, Fadar ta White House ta ce, “Shugaban Kasa na godiya ga wadanda suka kai daukin gaggawa wajen a lokacin da lamarin ya faru.”

Shugaban Hukumar Kashe Gobara na birnin na Pittsburgh, Frick Park, ya ce ko a watan Satumban bara sai da injiniyoyi suka yi aikin duba lafiyar gadar.