✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gadar Mina-Bida ta karye bayan kwana 5 da gyara ta

Gadar Sabon-Gida da ke hanyar Mina zuwa Bida a Jihar Neja ta sake karyewa kwana biyar bayan an kammala gyaran ta.

Gadar Sabon-Gida da ke hanyar Mina zuwa Bida a Jihar Neja ta sake karyewa kwana biyar bayan an kammala gyaran ta.

Karyewar gadar ta farko a ranar Litinin da ta gabata ta sa matafiya sun yi cirko-cirko, babu hanyar wucewa zuwa inda za su.

Lamarin ya sa dole masu zuwa halartar bikin cika shekara 70 na Etsu Nupe da aka shirya a ranar komawa gida.

A ranar Talata Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Jihar Neja (NIGROMA) ta yi aikin gyaran gadar, mai nisan kilomita 40 daga garin Bida.

Sai dai kuma bayan kwana biyar an sake komawa ’yar gidan jiya, gadar ta sake karyewa.

Wani direban motar haya, Idris Mohammed, ya ce matafiya sun koma yin yanke ta cikin kauyuka domin kauce wa gadar da ta karye.

Wasu kuma sun koma bin hanyar da ta tashi daga Bida zuwa Washishi ta bulla ta Zungeru domin zuwa Mina.

A shekarar 2018 ne dai gwamnati ta ba da aikin gyaran hanyar Mina zuwa Bida a kan Naira biliyan 24, amma har yanzu ba a kammala aikin ba.

Mun yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan Ayyuka na Jihar Neja, Mohammed Sani Lafiya, kan inda aka kwana a kan aikin, amma ba mu same shi ba.

Mun tuntubi kakakin ma’aikatar, amma ya shaida mana cewa an sauya masa wurin aiki zuwa wata ma’aikata ta daban.