✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gambiya: Sakamakon farko ya nuna Barrow na kan gaba

A sakamakon da aka fitar da sanyin safiya Barrow na da kuti'a 14,599

Sakamakon mazabun farko da aka samu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a Gambiya ya nuna cewa Shugaba Adama Barrow na kan gaba.

Barrow na fuskantar kalubale daga ’yan takara biyar, ciki har da tsohon maigidansa a siyasa, Ousainou Darboe.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito Shugaban Hukumar Zabe Alieu Momarr Njai yana cewa sakamakon mazabu hudu daga cikin 53 ya nuna Barrow na da kuri’a 14,599 yayin da Darboe ke da 6,188.

Nan gaba kadan ake sa ran samun sakamako daga lardunan kasar, bayan tattara alkaluman mazabu daban-daban.

Gambiya na amfani da wani tsarin kada kuri’a ne – inda masu zabe ke jefa tsakuwa a cikin garwar da ke dauke da hoton dan takarar da suke so.

Ana amfani da wannan tsarin ne don kauce wa lalata takardar kuri’a saboda adadin mutanen da ba su iya rubutu da karatu ba ya yi yawa.

Wannan ne dai zaben shugaban kasa na farko da aka gudanar tun bayan da aka tilasta wa tsohon Shugaban Kasa Yahya Jammeh tserewa daga kasar sakamakon turka-turkar da ta biyo bayan kayar da shi a zaben 2016.