✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gambiya ta fitar da Guinea daga gasar cin kofin nahiyar Afirka

Gambiya dai ta doke kasar Guinea da ci daya mai ban haushi.

A ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Kamaru a zagaye na biyu, kasar Gambiya ta fitar da kasar Guinea bayan ta yi nasara a kanta.

A yammacin ranar Litinin ne tawagar kasashen biyu suka kece raini, sai dai Gambiya ce ta yi nasara a kan Guinea da ci daya mai ban haushi.

Dan wasan gaban tawagar ta Gambiya, Musa Barrow, ne ya jefa kwallo a minti na 71, yayin wasan da aka fafata a filin wasa na Kouekong, da ke kasar ta Kamaru.

Har aka tafi hutun rabin lokaci dai, babu daya daga cikin kasashen da ta sami damar jefa kwallo a ragar abokiyar hammayarta.

Yanzu haka dai Gambiya ta samu tikitin zuwa zagaye na uku na gasar ke nan.