✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganawar Sheikh Gumi da ’yan bindigar Neja cikin hotuna

Ga hotunan ganawar Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da ’yan bindiga masu addabar Jihar Neja da makwabtanta inda ya shawo kansu suka amince su daina ta’asa.…

Ga hotunan ganawar Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da ’yan bindiga masu addabar Jihar Neja da makwabtanta inda ya shawo kansu suka amince su daina ta’asa.

Shugaban ’yan bindigar, Dogo Gide ya karbi nasihar malamin tare da alkawarin fara aiwatar da sulhun da malamin ya yi kira gare shi a dajin da ya hade Tegina a Jihar Neja da Birnin-Gwari a Jihar Kaduna.

Gaisawar Sheikh Gumi da wasu daga shugabannin ‘yan bindigar yayin da wasu daga cikinsu a kan babura ke kallo.
Wasu daga cikin yan bindigar a dajin da Sheikh Gumi ya kai wa ziyara
Malamin yana jawabi a lokacin ziyarar inda ya samu nasarar shawo kan yan bindigar.
Yan bindiga sun yi dafifi sun zagaye malamin a lokacin da yake nasiha a ziyarar da ya kai mafakarsu.
Sheikh Ahmad Gumi a kusa da wasu daga cikin yan bindigar da ke kan babur dinsu
Wasu daga cikin motocin da ke cikin tawagar malamin a gefen inda wasu daga cikin mutanen su.
Wasu daga cikin mutanen da aka samu dauke da makamai a cikin jejin.
Wani sashe na dajin da malamin ya shiga ya yi wa yan bindiga nasiha a Jihar Neja.