✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ganduje ba shi da hurumin tsoma baki a binciken Sanusi’

Wata kungiya mai fafutukar kawo daidaito a ayyukan gwamnati mai suna CAJA ta nuna damuwa  kan abin da ta kira yunkurin Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje…

Wata kungiya mai fafutukar kawo daidaito a ayyukan gwamnati mai suna CAJA ta nuna damuwa  kan abin da ta kira yunkurin Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na tsoma baki a binciken tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Hukumar Karbar Korafe-korafe da Hana Karbar Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) na binciken tsohon sarkin kan zargin badakalar wasu filaye mallakar Masarautar Kano a lokacin da Sanusi II ke kan karaga.

Sanarwar da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun jagorarta, Maryam Ahmad Abubakar, ta ce umarnin gwamnan ta bakin kakakinsa, Abba Anwar cewa hukumar ta ci gaba da binciken Sanusin ya saba dokar da ta kafa hukumar.

“A lokaci irin wannan, kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali wajen yaki da cutar coronavirus ko lalubo hanyoyin rage wa jama’a radadinta da kuma farfado da tattalin arzikin jihar da yanzu ya shiga mawuyacin hali.

“Maimakon hakan, ya bige da yin abubuwan da za su kawo rabuwar kai tsakanin al’ummar jihar, inji sanarwar.

CAJA ta kara da cewa matakin na Ganduje ya shafi kimar jihar da ma ta dattawan Arewa a idon duniya. Ta ci bada da cewa kalaman gwamnan kan dattawan jihar da na Arewa sun nuna karara cewa da ya fi so a ci zarafin tsohon sarkin fiye da a samu masalaha a rikicin.

A nasa bangaren kakakinsa gwamnan, Abba Anwar ya ce kalaman kungiyar soki-burutsu ne kawai, ko da yake tsarin dimokradiyya ya ba ta ‘yancin fadin albarkacin bakinsu.

Abban Anwar ya ce hukumar mai zaman kanta ce kuma cin gashin kanta take yi ba tare da kowane irin katsalandan daga bangaren gwamnati ba.

A cewarsa zargin ya nuna karara kungiyar ba ta fahimci sanarwar da gwamnatin ta fitar ba.

“A hukumance, tun da kotun daukaka kara ta yi fatali da bukatar sarkin kan dakatar da binciken sa, hakan na nufin kenan binciken zai ci gaba. Saboda haka gwamnati ba wai umarni ta ba su ba”, inji shi.