✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje da mai dakinsa ba su kamu da Coronavirus ba

Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat ya nuna cewa ba sa dauke da cutar, kamar…

Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat ya nuna cewa ba sa dauke da cutar, kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

A ranar Alhamis ne mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, ya sanar da manema labarai sakamakon gwajin da aka yi wa gwamnan.

“Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki game da wannan sakamako da ya nuna cewa ba sa dauke da cutar.

“Za mu ci gaba da addu’ar neman sauki ga dukkan wadanda sakamakonsu ya nuna suna dauke da cutar coronavirus, ba tare da la’akari da kasarsu ko kabilarsu ko jam’iyyar siyasarsu ko kuma addininsu ba.”

Gwamna Ganduje dai na cikin gwamnonin da a baya ko dai suka yi gum game da halin da suke ciki ko kuma ba a ma yi masu gwajin ba.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Kano ta dauki matakan hana coronavirus yaduwa wadanda suka hada da rufe iyakokin jihar.