✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje tauraro ne a siyasar Najeriya — Gwamnonin APC

An bayyana Ganduje a matsayin jagora na gari da ya jajirce don tabbatar da hadin kan al’umma.

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC (PGF) ta bayyana Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano a matsayin tauraro mai haske a siyasar Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar taya murnar da ta yi wa Ganduje yayin da ya cika shekaru 72 a duniya.

Gwamnan Jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar PGF, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai ranar Asabar a Abuja, babban birnin kasar.

Da yake jawabi, Bagudu ya ce Ganduje jagora ne na gari kuma mai hangen nesa da ya jajirce don tabbatar da hadin kan al’umma da kuma samar da Najeriya dunkulalliya.

Kazalika, Shugaban na kungiyar PGF ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin jagora na hakika la’akari da ayyukan da ya aiwatar domin ci gaban jam’iyyar APC.

Ya jaddada kudirin kungiyar wajen ganin da aiwatar da shirye-shiryen da ta sanya a gaba na bunkasa jihohinsu ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki, dakile rashin daidaito da kuma rage talauci.