✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya bi Shekarau har gida don kokarin ‘hana shi ficewa daga APC’

Ana ganin ziyarar na da nasaba da yunkurin Sanatan na ficewa daga APC

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, har gida, a daidai lokacin da alamu ke nuna Sanatan ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC.

Aminiya ta rawaito cewa Shekarau, wanda tsohon Gwamnan Kano ne ya kammala shirye-shiryen ficewa daga APC, inda ake sa ran a ranar Asabar zai sanar da komawar shi jam’iyyar NNPP a hukumance.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida yake dada kamari a jam’iyyar APC a Jihar ta Kano.

Ganduje da Shekarau dai sun sa labule yayin ganawar tasu da ta wakana da yammacin Juma’a.

Ko da yake ba a san me suka tattauna ba, wasu majiyoyi da ke da kusanci da Ganduje sun ce Gwamnan ya kai ziyarar ce don ya dakatar da Sanatan daga yunkurin shi na shiga NNPP, wacce tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake jagoranta.

“Yanzun nan ya fita. Sun shiga ciki sun tattauna, amma babu wanda zai iya fada maka me suka tattauna,” inji majiyar.

Daga cikin wadanda suka yi wa Gwamnan rakiya yayin ziyarar akwai Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da Kwamishinoni da sauran mukarraban gwamnan.

A ranar Juma’a ce dai Sanata Kwankwaso ya isa Kano a shirye-shiryen tarbar wasu kusoshin APC a Jihar.

Daga cikin wadanda suka fice don shiga NNPP akwai tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Alhassan Rurum da tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Sulaiman Kawu Sumaila.

Sauran sun hada da tsohon dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa da tsohon Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare a gwamnatin Ganduje, Nura Dankadai.