✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya cancanci yabo kan yaki da rashawa —Tinubu

Ya yaba yadda Gwamnan Kano, Abdullahi ke karfafa yaki da cin hanci a Jihar.

Jagoran jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, bisa abin da ya kira karfafa yaki da cin hanci a jihar.

Tinubu ya yaba wa Ganduje ne a lokacin kaddamar da ofishin Hukumar Karbar Koke-koken Jama’a da Yaki da Rashawa ta Jihar, a Kano ranar Lahadi.

“’Yan uwana ’yan Najeriya da sauran al’umma masu son ganin Najeriya da ma Afirka sun yi rabu da rashawa, yau rana ce ta musamman da aka ware domin cimma wannan muradi,” inji shi.

Ya ce samar da makamantan gine-gine na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kare martabar Najeriya a idon duniya a matsayin kasar da “ta yi bankwana da rashawa”.

Da yake mayar da jawabi, Ganduje ya yaba wa Shugaban Hukumar Barista Rimingado, yana mai ba da tabbatar bayar da duk gudunmuwar da ake bukata domin hukumar ta kai ga nasara.

Tsohon Gwamna Legas din, wanda ake hasashen zai nemi takarar Shugaban Kasa a 2023,  ya ziyarci Kano ne domin halartar taro na 12 da aka shirya na bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

A ranar Lahadin, Tinubu ya ziyarci Fadar Sarkin Kano, bisa rakiyar Gwamna Ganduje, a ranar Litinin kuma ake sa ran zai gana da sarakuna, ina da ranar ce za su yi Taron Majalisar Sarakunan Arewacin Najeriya.

Kafin zuwansa Kano, jagoran jam’iyyar ta APC ya ziyarci Jihar Katsina inda ya jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asara sakamakon gobarar da aka samu a Babbar Kasuwar Katsina, ya kuma ziyarci Fadar Sarkin Katsina domin gaisuwar ban girma.

Kafin zuwansa Katsina, sai da halarci Taron Shekara-shekara na Gidan Arewa da ke Kaduna inda ya yi jawabi.

Tun gabanin ziyararsa Kano ake ce-ce-ku-ce inda wasu matasan Kano suka yi wa gwamnan jihar kashedi da cewa kada ya sake a yi taron bikin cikar Tinubu shekaru 69 a Gidan Gwamnatin Jihar.