✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya dauki alarammomi aikin koyarwa

Gwamnatin Jihar Kano, ta dauki alarammomi 60 aikin koyarwa a makarantun tsangaya da ke jihar. Da yake mika wa alarammomin tarkadun kama aiki, Gwamna Abdullahi…

Gwamnatin Jihar Kano, ta dauki alarammomi 60 aikin koyarwa a makarantun tsangaya da ke jihar.

Da yake mika wa alarammomin tarkadun kama aiki, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukace su da su kara himmatuwa wurin koyar da ilimin Al-kur’ani.

Ganduje, yayin bikin rarraba kayan koyo da koyarwa na Naira biliyan 1.5 ga makarantun firamaren jihar, ya jaddada kudurin jihar na bunkasa ilimi a kowane mataki.

A nasu bangaren, alaranmomin sun bayyana godiyarsu ga Gwamnatin Jihar Kano bisa damar da suka samu kuma sun kuduri niyyar bawa mara da kunya.

Wasu daga cikin kayan da aka raba wa makarantun firamare na Jihar Kano.