✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya dawo da kwamishinan da ya dakatar bakin aiki

Ya dawo da Kwamishinansa da ya dakatar domin jagorantar babban aiki.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya dawo da Kwamishinansa da ya dakatar Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bakin aiki.

Ganduje ya dawo da Dan Sarauniya, wanda ya dakatar saboda zargin murnar mutuwar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, marigayi Abba Kyari, bakin aiki ne domin ya jagoranci akin bututun NNPC-AKK da ake gudanarwa.

“Alhamdulillah, ina kara farin dawowa cikin Gwamantin Ganduje a matsayin Shugaban aikin Bututun Mai na NNPC-AKK da kuma Kwamitin Masana’antu na Jihar Kano.

“Ayyukan biyu na NNPC da Jihar Kano za su zama harsashen sabbin cibiyoyin masana’anut da kasuwanci a jihar Kano karkashin gwamnatinsa”, inji Mu’azu a sakon da ya wallafa a shafinsa ranar Alhamis.

Idan za a iya tunawa a watan Afrilu ne Ganduja ya sallami Mu’azu, wanda shi ne Kwamishinan na Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Kano.

Gwamnan ya sallame shi ne bayan ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook da ya jawo zargin sa da murnar rasuwar Abba Kyari, tsohn Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai ya musanta zargin da cewa an yi masa gurguwar fahimta.

Dawo da shi aiki na zuwa ne a daidai lokacin da Ganduje da ya dawo da hadiminsa kan shafukan zumunta, Salihu Tanko Yakasai, wanda shi ma aka dakatar kan sukar Gwamantin Buhari da yin katabus a kan zanga-zanga #EndSARS.

A lokacin da ya wallafa sakon a farko-farkon zanga-zangar, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana karara cewa ra’ayinsa na kashin kansa ne.

Sai dai daga bisani gwamnatin jihar ta dakatar da shi daga aiki bisa hujjar cewa duba da matsayinsa a gwamnati, ba kasafai za a iya bambanta ra’ayin kashin kansa da matsayin gwamanti ba.