✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya gabatar da kasafin N245bn na 2023

Ganduje ya gabatar da kasafin kudi na karshe a matsayinsa na Gwamnan Kano.

Gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar daftarin N245bn a matsayin kasafin kudin jihar na badi.

Da yake gabatar da kasafin a ranar Juma’a, Ganduje ya ce ya mai da hankali ne kan karfafa gwiwa da ci gaban al’ummar jihar.

Ya kuma ce Gwamnati ta ware wa manyan ayyuka N39.1bn, sai bangaren samar da ruwan sha N15bn, da sufuri N8.6bn, da Noma N19.0bn, yayin da ayyuka da safayo zai lashe N35bn.

Ya ci gaba da cewa bangaren Ilimi ne ya samu kashi 27 na kasafin da ya yi daidai da N62bn, daidai da tsarin Kungiyar Kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).

Ya ce kasafin ya zo da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su daga darajar ilimi a kowanne mataki, musamman ma shirin gwamnatin na samar da iliimi kyauta, kuma dole.

Shugaban Majalisar, Alhaji Hamisu Chidari, ya bai wa gwamnan tabbacin zartar da kasafin ba tare da bata lokaci ba, tare da bukatar masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri don kare kasafin kudi a majalisar.

Kasafin dai shi ne na karshe da Ganduje zai gabatar a gaban Majalisar Dokokin jihar domin a watan Mayun badi ne zai kammala wa’adin mulkinsa.