✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya gargadi gwamnoni su guji raba kan jama’a

Ganduje ya shawarci kungiyar gwamnoni ta dage wajen hada kan Najeriya.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci gwamnonin kasar nan 36 da su hada kansu domin ganin an wanzar da hadin kai a kasar.

Yayin bikin murnar cika shekara 61 da samun ’yancin Najeriya da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, Ganduje ya ja hankalin takwarorinsa na sauran jihohi da su guji ce-ce-ku-ce su mai da hankali wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya.

“An zabi kowane gwamna ne domin yin aiki tare da takwaransa wajen wanzar da hadin kan kasa, kyakkyawan mulki da kuma fahimtar juna  domin ci gaban kasar baki daya,” in ji shi.

A wajen taron, gwamnan ya yabi dukkanin shugabannin kasar wadanda suka gabata saboda jajircewarsu wajen ganin cewa kasar ta samu ’yancin kai.

Daga karshe ya yi kira ga dukkanin al’ummmar Najeriya da su kasance masu bada ta su gudunmawar wajen gina kasar.