✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada manyan sakatarori 4 a jihar Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya nada nadin Manyan Sakatarori hudu a ma’aikatun gwamnati tare da kira a gare su da su kasance…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya nada nadin Manyan Sakatarori hudu a ma’aikatun gwamnati tare da kira a gare su da su kasance masu kwazo da jajircewa yayin sauke nauyin da ya rataya wuyansu.

Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Abba Anwar, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba.

Ya yi kira a gare su da su yi amfani da Fasahar Sadarwa ta zamani wajen kyautata ayyukansu, yana mai jaddada cewa, “dole ne ku bi ka’idoji mafiya kyau irin na manyan kasashen duniya a matsayinku na manyan jami’an gwamnati a jihar”.

Manyan jami’an gwamnatin hudu da aka daga likafarsu sun hadar da Fatima Fulani Sarki Sumaila, Umar Liman Albasu, Kabiru Sa’idu Magami da Abba Mustapha Dambatta.

Sanarwar ta ce gwamnan na umartar sabbin manyan sakatarorin da su kara himma da kiyaye martabar aikinsu tare da horonsu da su kasance abin koyi ga sauran kananan ma’aikatan gwamnatin masu tasowa.