✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada sabbin kwamishinonin zabe uku

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya nada sabbin Kwamishinoni uku a Hukumar Zabe ta jihar (KANSIEC)

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabbin Kwamishinoni uku a Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta jihar (KANSIEC).

Sabbin Kwamishinonin da Ganduje ya rantsar a ranar Talata su ne Muhammad Rufa’i, Idris Geza da kuma Aishatu Bichi.

Yayin zaman Majalisar Zartarwa da aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano inda aka rantsar da sabbin kwamishinonin, Ganduje ya ce yana sa ran za su ba da gudunmuwarsu wurin ganin an inganta zaben kananan hukomomin jihar na badi tare da tabbatar da adalci.

Ya shawarce su a kan riko da gaskiya da tabbatar da hadin kai a tsakanin sauran ma’aikatan hukumar wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ba tare da shakku ba.

Ganduje ya ce: “Ina kira ga sabbin kwamishinonin da aka nada su zama masu adalci ga kowa wurin gudanar da ayyukansu.

“Ba zan yi muku katsalandan ba wajen gudanar da harkokinsu kuma wajibi ne ku kasance masu adalci yayin sauke nauyin da rataya a wuyanku”.