✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada sabon Sarkin Rano

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Kabiru Muhammadu  Inuwa, Hakimin  Kibiya, a matsayin sabon Sarkin Rano. Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ya cike gurbin…

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Kabiru Muhammadu  Inuwa, Hakimin  Kibiya, a matsayin sabon Sarkin Rano.

Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ya cike gurbin da marigayi tsohon sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar ya bari bayan Allah Ya yi masa rasuwa a makon jiya.

tsohon sarkin Rano ya rasu ne cikin ‘yan awwani bayan an kwatar da shi a Asibiti,kuma zuwa wannan lokacin babu bayanin musababbin mutuwar sa.

Marigayin shine sarkin Rano na farko, bayan da gwamna Ganduje ya samar da karinmasarautu hudu masu daraja ta daya a jihar Kano.